Gwamnatin Kano Ta Yadda Zata Biya Wanda Ta Rushewa Shaguna
Gwamnatin Kano Ta Amince Za Ta Biya Diyyar Naira Biliyan Uku (3 Millions Naira) Ga Yan Kasuwar Filin Idi.
A ranar Alhamis ne gwamnatin jihar Kano ta amince ta biya diyyar Naira biliyan 3 ga ƙungiyar ’yan kasuwa masu shaguna a Masallacin idi, kamar yadda kotu ya umarta, sakamakon rushe shagunan ba bisa ƙa’ida ba.
An cimma wannan matsaya ne sakamakon wata buƙata ta neman sulhu da dukkanin ɓangarorin suka shigar gaban mai Shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya dake Abuja, a ranar 12 ga watan Disamba da kuma ranar 13 ga watan Disamba.
Idan za’a iya tunawa Idon Mikiya ta rawaito cewa, masu shaguna a filin masallacin idi sun shigar da ƙara nai lamba FHC/KN/CS/208/2023 a gaban kotun tarayya dake Kano, sakamakon umarnin da gwamna Abba Kabir Yusuf, ya bayar na rushe musu shaguna.
Masu neman takardar sun shigar da ƙara ga gwamnatin jihar, hukumar tsara birane ta jihar Kano; babban lauyan gwamnati, ‘yan sanda; Mataimakin Sufeto-Janar na ’yan sanda na shiyyar 1, Kano; Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano; Kwamandan hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya; da NSCDC, Jihar Kano.
Mai shari’a Samuel Amobeda na babbar kotun tarayya da ke Kano a ranar 29 ga watan Satumba ya umarci gwamnatin jihar da ta biya ‘yan kasuwar naira biliyan 30 a matsayin diyyar Naira biliyan 250 da ‘yan kasuwar suka nema na lalata musu kadarorinsu ba bisa ƙa’ida ba.
Amma sakamakon ƙin bin umarnin kotu da gwamnatin jihar ta yi, ‘yan kasuwar sun shigar da kara mai lamba FHC/ABJ/CS/1382/2023 a gaban mai shari’a Ekwo, inda suka buƙaci a tilastawa gwamnatin ta biya su kuɗaɗen ko kuma a rufe asusun gwamnatin kuma kotun ta bada umarnin rufe wasu asusun gwamnatin jihar dake wasu bankuna sama da guda 20.
Har ila yau, sun danganta asusu da ke hannun waɗanda aka yi garkuwa da su zuwa Naira biliyan 30 don gamsuwa da hukuncin da aka yanke a ranar 29 ga watan Satumba, da sauran sassa, kuma mai shari’a Ekwo ya amince da buƙatar a ranar 28 ga watan Nuwamba.
Wasu daga cikin waɗanda suka shiga cikin wannan ƙara sun haɗa da Babban Bankin Najeriya, Akanta Janar na Tarayya, Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya, FAAC, UBA, Bankin Zenith, Bankin Unity, Bankin Polaris, da dai sauransu.
Sai dai kuma da aka ci gaba da sauraren ƙarar a ranar Alhamis, lauyan masu ƙarar (’yan kasuwa), Dokta N. A. Ayagi, ya shaidawa kotu cewa sun samu fahimtar juna tsakanin su da waɗanda suke kara.
“Mun sami fahimtar juna tsakanin mu da waɗanda muke ƙara wato gwamnatin jihar Kano, kuma dukkanin mu mun aminta da yarjejeniyar da muka cimma.” A cewar Ayagi