Kannywood

Gwamnatin Kano Ta Haramta Nuna Shirin Kwana Casa’in Da Gidan Badamasi Arewa24

Gwamnatin Kano Ta Haramta Nuna Shirin Kwana Casa’in Da Gidan Badamasi Arewa24

Gwamnatin Jihar Kano ta umarci tashar talbijin ɗin nan mai farin jini ta Arewa24 da ta dakatar da nuna wasu shirye-shiryen dirama masu dogon zango guda biyu da ta ke nunawa, wato ‘Gidan Badamasi’ da kuma ‘Kwana Casa’in’. Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta jihar ce ta aika wa gidan talbijin ɗin da umarnin a cikin wata takarda mai ɗauke da kwanan wata 7/4/2020.

Shugaban hukumar, Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallah), shi ne ya rattana hannu a kan takardar.

Dakatar da waɗannan finafinan ya faru ne saboda hukumar ta ce ba ta duba su ba ake haska su.

Hukumar ta ce ƙin ba ta wasannin domin ta tace su ya saɓa wa dokar ta. Ta nemi a dakatar da haska su har zuwa lokacin da aka cika ƙa’idar ta.  Su dai waɗannan finafinai biyu, su na da ɗimbin masu kallon su a duk faɗin duniya saboda tasirin su ga masu kallo.
A yanzu babu wani wasan talbijin da ake kallo a arewacin Nijeriya da duk inda ake jin Hausa kamar su.  A cikin wannan satin ne aka shiga zango na biyu na shirin ‘Kwana Casa’in’, to amma tun da aka fara nuna shi jama’a su ka fara yin ƙorafi dangane da yadda salon sa ya canza.

Mujallar Fim ta fahimci cewa da man ko a can baya ana ganin kamar shirin ya na tona asirin gwamnati ne, don haka ake ganin babu mamaki idan gwamnatin Kano ta yi amfani da hukumar tace finafinan domin a dakatar da shi.  Mujallar Fim ta tuntuɓi wani jami’in Arewa24 ya furta wani abu a kan wannan abu da ya faru, sai ya ce ba hurumin sa ba ne amma hukumar gidan ce za ta ce wani abu.

Ya zuwa lokacin wallafa wannan labari dai hukumar gidan talbijin ɗin ba ta ce komai ba dangane da wannan dokar da aka ƙaƙaba mata.  Abin da jama’a su ka zuba ido su gani shi ne yadda wannan doka za ta yi tasiri a kan gidan talbijin ɗin, wanda ake ganin kamar ya fi ƙarfin Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano.

Daga @kannywood_fimmagazine

NgHausa

I am YusHau Uba, CEO/Founder Of HausaMini.Com.Ng
Back to top button