E News

Gwamnati Zata Biya Malaman Jami’a Kudadensu

Gwamnatin Tarayya Ƙarƙashin Jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu Ta Fara Biyan Malaman Jami’a Albashin Da Gwamnatin Baya Ta Riƙe Musu

Majiyoyi daban-daban daga ɓangaren ƙungiyar malaman Jami’ar, (ASUU) sun tabbatar da fara samun albashin nasu a wannan rana ta Litinin.

“Gaskiya ne gwamnati ta fara biyanmu haƙƙoƙinmu”. Cewar Farfesa Gbolahan Bolarin, shugaban ƙungiyar malaman Jami’a, (ASUU) reshen Jami’ar fasaha ta gwamnatin tarayya da ke garin Minna, Jihar Neja.

A watan Oktoba, 2023, shugaban ƙasa Tinubu ya amince a biya malaman haƙƙoƙinsu na wata huɗu cikin watanni takwas da aka riƙe musu.

Gwamnatin tarayya ta shugaban ƙasa Buhari da ta gabata, ita ce ta riƙe albashin Malaman bisa abin da ta kira da “ba aiki, ba biya” sakamakon dogon yajin aikin watanni takwas da suka tsunduma a shekarar 2022.

Tun da farko, ministan ilimi, Tahir Mamman, ya bayyana cewa tuni gwamnati ta ƙara albashin ma’aikatan jami’ar da kaso 35.

Kazalika, ministan ya ƙara da cewa gwammati ta kuma ba wa jami’o’i ƴancin cin gashin kansu ta hanyar cire su daga tsarin biyan albashi na baiɗaya (IPPS). Inda ya ƙara da cewa yanzu Jami’o’i sun samu ƴanci ba sa buƙatar neman izini kafin su ɗauki aiki ko cike wasu gurabe na ma’aikata.

Hakan ya biyo bayan yarjejeniyar da aka cimma ne a hukumance da ƙungiyoyin Malaman manyan makarantun gaba da sikandire. Cewar ministan.

Back to top button
error: Content is protected !!