E News

Gwamnati Bata Da Shirin Girke Sojojin Kasashe

Gwamnatin Tarayya Bata Da Shirin GirKe Sojojin Kasashen Waje A Nigeria.

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Alh. Idris Malagi ta yi watsi da rade-radin da ke yawo cewa Gwamnatin Shugaba Tinubu na da shirin bai wa sojojin kasashen waje matsuguni a Najeriya.

Sanarwar ta yi kira ga daukacin ‘yan kasa da su yi watsi da wannan jita-jitar inda ta tabbatar da cewa babu wani shiri ko tattaunawa da Gwamnati ke yi da wata kasa da niyyar samar da sansanin sojojin kasashen waje a Najeriya.

Sanarwar ta kara da cewa dama can gwamnatin Najeriyar ta gaji samun hadin kan kasashen ketaren wajen tunkarar kalubalen tsaro da ke addabar kasar, kuma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da jajircewa wajen zurfafa wannan kawance, da nufin cimma manufofin tsaron kasa wanda suna cikin ajandarsa ta sabunta fata na gari.

Back to top button
error: Content is protected !!