E News

Gwamna Uba Sani Zai Raba Bilyan 4.2Bn Ga Al’ummar Jihar Kaduna

Gwamna Uba Sani Zai Raba Kudade Naira Bilyan 4.2Bn Ga Al’ummar Jihar Kaduna Domin Rage Radadin Cire Tallafin Man Fetur.

Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya bayyana cewa nan da kwanaki masu zuwa sama da mutum 4000 masu ƙananan sana’o’i da gwamnatin jihar Kaduna ta tantance ciki har da sauran marasa galihu da aka sanya a cikin shirin “Financial Inclusion” za su ci gajiyar tallafin N4.2billion domin rage radaɗin rayuwa biyo bayan cire tallafin man fetur da hauhawar farashin kayayyaki da ake fuskanta

Gwamna Sani ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na TVC a ranar 19 ga Fabrairu, 2024, inda ya amsa tambayoyi da suka hada da halin da ake ciki na tattalin arziki a Najeriya, tashin farashin abinci, tsadar rayuwa, da kokarin da gwamnatinsa ke yi na inganta tattalin arzikin kasar da rage wahalar rayuwa ga al’ummar jihar Kaduna.

Da yake amsa tambayoyi game da yadda ƴan ƙasa ke zanga-zanga a baya-bayan nan na nuna rashin amincewa da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki a yanzu, Gwamna Sani ya bayyana cewa, “Babu wata tada zaune tsaye a jihar Kaduna kan wannan batu, domin mun yi aiki da kungiyoyin kwadago, mata ƴan kasuwa da ma kungiyoyi masu zaman kansu, saboda Ni ma ɗan gwagwarmaya ne.

Tun Kafin faruwar tada waɗannan jijiyoyin wuya, na hikayo faruwar hakan shi ya sa ni kadai ne Gwamna da ya rattaba hannu kan wata doka ta zartaswa kan hada-hadar kudi, don sanya mutum 2.5 marasa galihu miliyan cin gajiyar duk wata dama tatallafin kuɗi.

Haka kuma mun tsamo ƙananan yan kasuwa mutum 4200 a Jihar Kaduna kuma nan da mako guda mun yanke shawarar tallafa musu da kayayyakin tallafi da ya kai kimanin Naira Biliyan 4.2, wanda kuma zai isa kai tsaye ga marasa galihu da wasu kananan ‘yan kasuwa.

Bugu da kari, sama da mutane miliyan 1.5 yanzu ake da’awa da su a ada-hadar kuɗu tun bayan lokacin da muka rattaba hannu kan dokar hada-hadar kudi a jihar Kaduna” Gwamna Sani ya ce.

Gwamna Sani ya bayyana cewa shirin hadin gwiwa ne na masu ruwa da tsaki kamar kungiyoyin kwadago, matan kasuwa, masu fama da nakasa, kananan manoma, shugabannin addini da na al’umma.

“Mun himmatu a jihar Kaduna, shi ya sa kungiyar kwadago ke goyon bayan abin da muke yi saboda muna gudanar da gwamnati a buɗe.

Tun kafin gabatar da kasafin kudin ga Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, mun gudanar da tarukan ganawa da al’umma inda na shaida musu cewa ba za mu iya yanke shawara kan abin da za mu yi wa mutanen Kaduna ba, ba tare da gudummuwarsu ba. Har ila yau, a tarukan mun jaddada kudurin tafiyar da gwamnati a bude, shi ya sa muka ware Naira Biliyan 22 don noma irinsa na farko a tarihin Kaduna, kuma hakan ya samo asali ne daga irin gudunmawar da muka samu kai tsaye daga wajen jama’armu, shi ya sa muka ware kaso mai tsoka kasafin kudin akan harkar noma. Wannan yasa muke samun fahimtar juna da mutanen da muke Mulka”, Gwamna Uba Sani .

Back to top button
error: Content is protected !!