Gwajin Lafiyan Daya Kamata Ayi Kafin Aure
Gwajin lafiya da ya kamata a yi kafin aure da ya fi yin ”Pre Wedding Picture” muhimmanci
A wannan zamanin babu wani abu da yi fi burge matasa musamman masu shirin yin aure da ya wuce yin tsala-tsalan hotuna da ake kira ”Pre-Wedding Pictures”.
Sabon tsari ne da ya ɓulla daga ƙasashen da suka ci gaba, sai dai mamayar da shafukan sada zumunta suka yi wa duniya ya sa kowa ma ya rungumi wannan al’ada, ciki har da ƙasashe masu tasowa irin Najeriya.
Yin hotunan kafin aure a yanzu ya zama kamar ɗaya daga cikin farillan auren, inda mutane kan kashe kuɗi mai yawa da ɓata lokaci wajen yin su.
Masu ɗaukar hoto na zamani kan caji sabbin ma’auratan daga naira 20,000 har zuwa naira 50,000 don ɗaukarsu, kamar yadda wasu shahararrun masu hoto a Kano da Abuja suka shaida mana.
To sai dai masana harkar lafiya na cewa yin gwaje-gwajen lafiya sun fi muhimmanci sau 100 kafin aure fiye da yin hotunan.
A wannan maƙala ta musamman, BBC ta yi duba ne kan waɗanne ne irin gwaje-gwajen da ya kamata a yi kafin aure, nawa za a biya a yi su kuma mene ne muhimmancinsu.
Dr Ibrahim Musa wani likita ne a asibitin Koyarwa na Malam Aminu AKTH da ke Kano a arewacin Najeriya, ya kuma jaddada cewa da masu shirin aure sun san muhimmanci waɗannan gwaje-gwaje da taimakon da za su yi wa zamantakewarsu, da ba su yi wasa da su ba.
Likitan ya ce shi tsarin da ake yi na bincike kafin aure ga ma’aurata yana da ƙa’idoji da bangarori da dama.
- Na farko ana so a tabbatar da cewa ma’auratan ba su cutar da juna ba a wurin mu’amala ta auratayya
- Na biyu ana so a tabbatar da yaran da za a haifa ba su cutu daga su iyayen ba ta hanyar gadon wani ciwo da yake iya yaɗuwa daga iyaye.
”Amfanin wannan gwaji shi ne don a rage yaɗuwar wasu cututtuka da ke bazuwa ta hanyar zaman aure, don a samu ci gaba mai ɗorewa tare da taimaka wa gwamnati wajen rage kashe kuɗaɗe a fannin lafiya kan irin waɗannan cututtukan,” in ji likitan.
Sai dai ya ce ko wacce ƙasa ta kan duba wane tsari ne ya fi dacewa da ita da irin cututtukan da suka fi addabarta sai masu niyyar auren su yi gwaje-gwajen da suka danganci hakan.
Ga wasu daga gewaje-gwajen da ya kamata masu niyyar aure su dinga yi a Najeriya:
Gwajin jini na cutar sikila
Kusan kaso biyu ko uku na mutanen Nijeriya suna da ciwon sikila, yana yaɗuwa ne ta hanyar auratayya tsakanin mace da namiji da suke da nau’in na ciwon da a ke kira career.
To su kuma career din nan suna nan a cikin jama’ad. Kowane mutum daya cikin hudu a Najeriya yana dauke da nau’in ciwon, wato kaso 25 kenan na ƴan Najeriya career ne.
Don haka kafin a yi aure idan aka gwada aka tabbatar cewa shi namijin career ne matar career ce, wannan sai a ce bai kamata su yi aure ba, kun ga an rage wa al’umma da gwamnati da kowa ɗawainiyar rashin lafiyar yara masu sikila.
Gwajin cutar HIV/AID, STD da Hepatitis B da C
A kan so kafin a yi aure a yi gwaji na waɗannan cututtuka da suke yaɗuwa ta hanyar jima’i.
Waɗannan cututtuka ne da za a iya daukar su ko namijin ya dauka ko matar ta dauka daga namijin idan dai akwai mai shi a cikinsu.
Don haka idan daya a cikinsu yana da shi sai a ba su magani su warke kafin auren, wadanda kuma ba a warkarwa sai a ba da shawara ka da su yi aure don gudun cutar da daya daga ciki.
Gwajin rukunin jini:
Gwajin rukunin jini ga masu shirin aure yana da fa’ida, saboda a wani lokaci idan aka samu bambanci na nau’in jini tsakanin uwar da kuma jariri ko jaririya, ana iya samun matsala wani lokaci yara su zo da ciwon nan da ake kira jondis, wato matsananciyar cutar shawara, wanda idan an haihu za a ga idon yaron ya yi kamar rawaya, sannan kuma jikinsa ma ya sauya launi ya zama rawaya saboda jikinsa yana farfashewa.
Wannan yana faruwa ne a dalilin bambanci a tsakanin rukunin jinin mahaifiya da kuma na yaron. Wani lokaci akwai wani rukuni na jini da ake kira RH, idan uwar tana da RH da ya zama korau (negative) shi kuma yaron na shi ya fito tabbacecce (positive).
Wani lokaci kuma ana samun matsalar haihuwar jarirai da jondis idan ya kasance uwar tana da rukunnin jini O kuma jaririn ya zamanto yana da rukunin jini A ko B ko AB.
Gwajin cutar HIV/AIDS
Shi ma wannan gwaji ne mai matuƙar muhimmanci da ya kamata a yi kafin aure, don hana yaɗa cutar mai karya garkuwar jiki ga wanda ba shi da ita.
Idan har aka samu cikin masu shirin yin auren ɗaya na ɗauke da ita, to ya kamata su ga likita don samun shawarwarin likitoci kan mataki na gaba da ya kamata su bi don gudun yaɗuwar cutar.
Gwajin lafiyar ƙwaƙwalwa
Likitoci sun bayyana cewa wannan gwaji ne mai matuƙar muhimmanci ga masu niyyar aure. Sun bayyana cewa a kan yi saurin gane wasu yanayin na rashin lafiyar ƙwaƙalwa da mutum ke ciki, amma a mafi yawan lokuta sai an yi gwaji.
Ƙwararru sun kuma ce rashin yin gwajin kan haifar da gagarumar matsala a wasu lokutan ta yadda sai bayan auren hakan ke tasowa.
Kazalika rashin lafiyar ƙwaƙwalwar kan zama na gado a lokuta da dama, inda bayan an yi aure abin kan shafi yaran da za a haifa.
Dukkan waɗannan gwaje-gwaje dai a cewar masana lafiya ba sa cin wasu kuɗaɗe na a zo a gani.
Sannan a baya-bayan nan an samu ci gaba sosai inda a arewacin Najeriya alal misali, wasu masallatan ma da yanzu aka fi ɗaura aurarraki a acan, su kan nemi sai an nuna musu shaidar wasu muhimman gwaje-gwajen lafiyar kafin a ɗaura auren.
@BBCHausa