Gudunmawar Sanata Barau Wajen Magance Matsalolin Arewa
Gudunmawar Sanata Barau Jibril (Maliya) Wajen Magance Matsalolin Arewa Maso Yammacin Najeriya.
Daga cikin muhimman ƙudurai da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Barau I. Jibrin Maliya ya ɗauki nauyin kawowa gaban Majalisa, akwai ƙudurin samar da Hukumar Bunƙasa Arewa maso yammacin Najeriya (NWDC). Manufar wannan ƙudurin shine samar da tallafi na musamman da zai magance matsalolin da suke addabar wannan yankin.
Kamar yadda yake sanannen abu wajen ɗan Najeriya, yankin Arewa maso yamma na fuskantar matsaloli da suka haifu sakamakon ayyukan ta’addanci da yan bindigar daji, mahara, ɓarayin daji, ƴan fâshi da mâkâmi, masu gârkúwa da mutane da yan B0k0 Háram suka haifar, wanda suka jawo koma baya a fannoni daban-daban na cigaban yankin.
Sanata Barau yayin gabatar da wannan ƙudurin na kafa Hukumar ta Bunƙasa Arewa maso yammacin Najeriya, ya bayyana cewa;
”Arewa Maso Yamma a matsayin sa na yanki ya bada gudummawa sosai wajen ci-gaban Najeriya musamman a fannin noma da sauran abubuwan da suka shafi cigaban ƙasar nan, amma har yanzu yankin na fama da mummunan koma baya”
”Abinda yankin yake buƙata a yanzu shine Gwamatin Tarayya ta tallafa wajen samar da hanyoyi da kayayyakin inganta rayuwa da ilimantar da ɗimbin matasan yankin tare da samar da hanyoyin bunƙasa yankin gaba ɗaya ta yadda zai bunƙasa kamar ko fiye da sauran shiyyoyin kasar nan”.
”Ta’asar yan ta’addan bindiga da masu garkuwa da mutane sun yi matuƙar lalata ababen inganta rayuwa a sassan yankin, lamarin daya jawo ficewar masu zuba hannun jari da yan kasuwa da masu gudanar da kamfanoni da ma’aikata daga yankin. Wannan ya jawo muguwar illa ga harkokin tattalin arzikin yankin, tare da ƙarancin abinci da rashin aikin yi, wanda a baya yankin yayi ƙaurin suna wajen noma da siyar da kayan abinci a yankin Sahel”
”Don haka, wajibi ne Gwamnatin Tarayya ta mayar da hankali wajen magance waɗannan matsaloli da ƙalubale da suka addabi yankin Arewa maso yamma a gaba ta hanyar kafa Hukumar Bunƙasa Arewa maso yamma, domin kawo ɗauki wajen magance matsalolin da suka addabi yankin tare da yin duk abinda yankin yake da buƙata”.
Wannan ƙuduri zamu iya cewa shine abun alkairi mafi girma da Arewa maso yamma ta samu tun farkon wannan Majalisa ta 10, kuma zai shawo kan kaso mafi yawa na matsalolin da suka addabi yankin musamman a fannin ilimi, kiwon lafiya, tsaro, kasuwanci, noma da kuma tattalin arziƙi.
Wannan ƙudurin zai taimaka wajen dawo da masana’antun da ke ficewa daga jihohin yankin, su dawo su cigaba da gudanarwa a yankin, zai kuma kara yawaita ayyukan yi ga matasan jihohin wanda a yanzu kaso mai yawa na su ke zaune babu wadatattun ayyukan da zasu yi.
Bisa dukkan alamu kuma kwalliya ta biya kuɗin sabulu, domin ƙudurin ya samu goyon baya daga yan majalisar dattijai har 20 daga yankin Arewa maso yammacin kasar nan da ma ragowar yankunan, kuma tuni anyi karatu na 2 a gaban Majalisar. Hatta shugaban majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio ya goyi bayan kudirin inda ya bayyana cewa yankin na da tarin jama’a kuma buƙatar a bunƙasa yankin, abu ne da dace.
Kamar yadda yankin Neja-Delta suke da hukumar bunƙasa yankin Neja-Delta, yankin Arewa maso Gabas ke da Hukumar bunƙasa Arewa maso gabashin Najeriya, wanda duka aka samar da su saboda wasu matsaloli da suka kawo cikas ga cigaban su, kuma samar da hukumomin ya haifar da abinda bahaushe ke kira ‘ɗa mai ido’, to tabbas samar da Hukumar a arewa maso yamma zai zama cigaba mai ɗorewa da za a mora a yankin da ma Najeriya baki daya.
Allah ya taimaki Sanata Barau Jibrin Maliya, Allah ya taimaki Yankin Arewa maso yammacin Najeriya, Allah ya taimaki Najeriya. Ameen
~Aliyu Samba
Mataimaki na musamman ga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya a kafafen sada zumunta.
2/6/2024