Labarai

GasKiyar Magana Game Da Rushe Gidan Rarara

GasKiyar Magana Game Da Rushe Gidan Mawaki Dauda Kahutu Rarara Da Gwamna Ganduje Akace Yasa A Rushe Bisa Zargin Cewa Anyi Gidan Ba Akan Qa’ida Ba.

GasKiyar Abin Dake Faruwa Shine, Zuwa Yanzun Dai Ba.a Tabbatar Da Rushe Gidan Mawakin Ba, Gwamnatin Kanon Dai Ta Fitar Da Sanarwar Cewa Duk Wani Gini Da Aka Yishi Kan Hanyar Magudanar Ruwa, Ko Hawa Nawa Ne, Sai Mun Rusheshi. Mutum Kuma Yayi Asara Kenan Cewar Dr. Abdullahi Umar Ganduje Gwamnar Jihar Kano.

Akwai Sanarwar Da Aka Fitar Kwanaki Inda Akace Cikin Gidajen Da Ayisu Ba Akan Qa’ida Ba Sun Hada Da Gidan Mawakin Dauda Rarara Kahutu, Inda Ake Ganin Da Yiwuwar Aiki Kai Har Kan Gidan Mawakin.

Sai Dai Kuma Da Yawan Mutane Suna Tunanin Kamar Cewa Wannan Mataki Da Gwamnatin Kano Da Dauka Tana So Tayi Amfani Da Damarta Ne Dan Muzantawa Mawakin, Tunda Ana Zargin Cewa Yanzun Ba.a Ga Maciji Tsakanin Mawakin Da Gwamnatin Jihar Ta Kano.

Back to top button