Kannywood

GasKiyar Abin Daya Faru Da Jaruma Maryam CTV

GasKiyar Abin Daya Faru Da Jaruma Maryam CTV Game Da Hatsatin Da Tayi.

KWANAN nan wani labari ya bazu a soshiyal midiya cewar jarumar Kannywood, Hajiya Maryam Sulaiman (Maryam CTV) ta yi haɗari.

Maryam CTV

Haɗarin ya faru a ranar Asabar da ta gabata, 10 ga Fabrairu, 2024.

Labarin ya ɗauki hankalin mutane sosai saboda irin yadda aka riƙa bayar da labarai masu karo da juna da kuma ƙarin gishiri a game da abin ya faru.

Wasu sun riƙa cewa jarumar ta karairaye a hannu da ƙafa, wasu kuma su ce ƙafafun ta ne suka yi rugu-rugu, har ba ta san ma halin da take ciki ba, da dai sauran su.

Domin jin yadda gaskiyar labarin, wakilin mujallar Fim ya samu ganawa da Hajiya Maryam CTV a gidan ta da ke unguwar Hotoro a Kano inda ya same ta a zaune a kan kujera a falon ta tare da masu zuwa duba ta.

Mun tambaye ta ko me ya faru da ita kuma a wane hali take ciki a yanzu?

Hajiya Maryam ta amsa: “To gaskiya abin da ya faru da ni shi ne, a ranar Asabar ɗin da ta gabata, da misalin ƙarfe ɗaya na rana, na fita unguwa a kan Adaidaita Sahu, Keke Napep.

“To, ka san dai kowane mutum a duniya da irin ƙaddarar sa, kuma in dai mutum yana raye zai riski ƙaddarar sa. To kuma alhamdu lillahi ƙaddara ta sauka a kai na amma kuma ta zo da sauƙi, ba kamar yadda mutane suke ta yaɗawa ba.

“Ƙaddara ce ta tsautsayi. Na hau ɗan Adaidaita Sahu zan je Zoo Road, a daidai Kwanar Sabo da ke Hotoro wani mai moto ya zo ya daki bayan Adaidaita Sahun da muke ciki ni da ƙawa ta, to shi kuma Adaidaita Sahun da muke ciki sai ya daki wata mota, sai ya faɗi da mu ya juya, wanda sakamakon wannan abin sai ƙarfen Adaidaita Sahun ya danne mini hannu, shi ne na samu karaya a hannu na na hagu waje biyu, wanda a yanzu halin da na samu kai na a ciki kenan.”

Dangane da masu cewa ta samu karaya a hannu da ƙafa, duk ta karairaye, kuma ba ta san ma a inda ta ke ba, ta ce, “To gaskiya ba haka ba ne, don kai ma a yanzu kana tare da ni a yanzu muna magana ba kamar yadda ake faɗa na kakkarye hannu da ƙafa ba, don ƙafa ta babu karayar komai, sai dai ɗan ƙujewa irin na faɗuwa da kuma hannu na na dama.

“Amma wannan karayar ta hannun hagu shi ne dai ciwon da na samu. Ban kakkarye rugu-rugu ba. Saboda ana ta bugo mini waya daga garuruwa da dama, har ma daga Nijar da sauran wasu ƙasashe ana tambayar cewa na samu ciwo na karairaye na fita hayyaci na, ban san kowa a kai na ba.

“Wallahil azim ƙarya ne! Ko lokacin da abin ya same ni a cikin hayyaci na na ke, na san abin da na ke yi har muka je asibiti aka yi mini aiki sannan aka kai ni wajen ɗorin gargajiya aka yi mini babu abin da na manta, babu kuma abin da ban sani ba.”

Da mu ka tambaye ta a inda take a yanzu, sai ta amsa da cewa: “A yanzu ina gida na kamar yadda ka zo ka same ni, saboda ka ga ɗorin gida aka yi mini, kuma sakamakon ba mai tsanani ba ne sosai ka ga wajen da na karye ɗin, tsakiyar hannu ne tsakanin gwiwar hannu zuwa gaba; duk kusan a waje ɗaya ne, karayar su na kusa da kusa, don ɗayan ma sai da ƙashin ya bulluƙo, sai da aka mayar da ƙashin aka yi ɗinki sannan aka zo aka yi ɗorin.

“Kuma ina sa ran nan gaba kaɗan za a samu sauƙi da yardar Allah. Don ka ga ko zama ban yi ba a asibitin, sun duba ni ne su ka yi mini aikin da za su yi su ka ba ni magunguna da allurai.

“Kuma sai aka yanke shawarar a je a yi ɗori na gargajiya. Don haka na je Ƙofar Na’isa gidan Sarkin Maɗora, a nan ‘ya’yan sa su ka yi mini ɗorin. Kuma a cikin ‘ya’yan sa ma akwai likita, don shi ne ma ya mayar mini da wannan ƙashin da ya bulluƙo ya gyara sannan ya ɗinke, sai su ka zo su ka yi ɗorin daga baya.

“Don haka saƙo na ga masoya na, don Allah ku kwantar da hankalin ku. Na san irin wannan abin da tashin hankali. Duk wanda ka ke so ba ka son wata masifa ko bala’i ya same shi. To don Allah a yi haƙuri abu ne na ƙaddara kuma ya faru kuma da yarda Allah za a samu sauƙi.

“Don haka ina godiya ga dukkan waɗanda su ka damu da halin da na ke ciki su ke ta bugo wayoyi da saƙon kar-ta-kwana da na WhatsApp daga ƙasashe da dama daga gari-gari.

“Kuma godiya ga masu zuwa gida su na duba ni, wanda tun daga ranar da abin ya faru har zuwa yanzu kullum jama’a zuwa su ke yi daga safe har zuwa dare. Na gode. Allah ya saka da alheri.”

Daga- Fimmagazine.com

Back to top button
error: Content is protected !!