Ganduje Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Darakta Aminu S. Bono
SHUGABAN jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana rasuwar darakta a Kannywood, Aminu Surajo Bono, da cewa babbar asara ce ga masana’antar shirya finafinan.
Aminu dai ya rasu ne a jiya ba zato ba tsammani sakamakon ciwon ciki, a cewar iyalan sa.
An yi jana’izar sa a safiyar yau Talata.
Mista Edwin Olofu, babban sakataren yaɗa labarai na shugaban jam’iyyar ta APC, ya faɗa a takardar da ya raba wa manema labarai a yau a Abuja cewa Ganduje ya bayyana matuƙar kaɗuwa kan rasuwar fitaccen daraktan kuma jarumi.
A takardar wadda mujallar Fim ta samun kwafen ta, ya ce mutuwar Aminu ta faru a daidai lokacin da masana’antar ke matuƙar buƙatar sa.
Ganduje, wanda tsohon gwamnan Jihar Kano ne, ya ce: “Bono ya kasance rimi kere itace a cikin masana’antar finafinan wajen sadaukarwar sa ga tabbatar da ganin an kare al’adu da kyawawan ɗabi’un da Hausawa da Fulani su ka gada.”
Ya ce rayuwar Bono a industirin ta yi kyakkyawan tasiri, kuma ta taimaka ƙwarai da gaske wajen jawo wa industiri farin jini.
Ganduje ya ce: “Ina so in yi amfani da wannan dama in yi wa musamman iyalan sa gaisuwa, tare da su kan su ‘yan Kannywood baki ɗaya a kan wannan rashin da aka yi na ɗaya daga cikin haziƙan industirin, wato babban darakta Aminu Surajo Bono.”
Ya ƙara da cewa, “Rayuwa da kuma zaman Bono a masana’antar shirya finafinan ta kawo ƙarin daraja ga Kannywood.”
Ganduje ya ce rayuwar marigayin a cikin industiri da wajen ta ta ƙara ƙauna a ran waɗanda ra’ayin su ya sha bamban game da industirin.
Shugaban jam’iyyar ya ce, “Ya zama tilas in ce rasuwar Aminu Surajo Bono ta samar da giɓi a masana’antar, kuma wannan gaskiya ce da za mu ci gaba da zama da ita a shekaru masu zuwa.”
Ganduje ya yi addu’ar Allah ya ba iyalan daraktan da dukkan Kannywood haƙurin jure wannan babban rashi, sannan ya roƙi Allah da ya gafarta masa dukkan kurakuran sa, ya yi masa sakayya da gidan Aljannar Firdausi, amin.
Daga Shafin: Fimmagazine.com







