Labarai

Game Da Azumin Awa 3 A Ƙauyen WEKAN na Ƙasar Oman

Ba wannan ne karo na farko ba, kusan duk watan Azumin Ramadan tun daga shekarar 2015 sai an yaɗa labarin ƙauyen WEKAN na Ƙasar Oman a matsayin garin da ake azumin tsawon awanni 3 kacal daga hudowar rana zuwa faduwar ta. Har wasu ma cikin masu yaɗa labarin ke marmarin ina ma da ko za su samu hanyar tafiya can don samun sauƙin Azumin musamman a lokutan da ake matsanancin zafi a yankin Sahara.

MENE NE GASKIYAR LAMARIN?

Wekan_Village 01

Wekan_Village 02

Wekan_Village 03

Wekan_Village 04

Wekan, wani ɗan tsibirin ƙauye ne da ke da tazarar nisan kilomita 150 daga babban birnin Ƙasar Oman wato Muscat ta ɓangaren yamma. Ƙauye ne da mafi sauƙin abun hawan da za ka yi amfani da shi zuwa cikin sa shine Jakuna da Dawakai da kuma manyan motoci masu iya keta duwatsu da kwazazzabai (a shekarar 2013 kenan) amma a yanzu an samar da hanyar mota mai kyau har cikin ƙauyen a dalilin tambarin da sunan garin ya yi a duniya dalilin jita-jitar da ake ta yaɗawa na azumin awanni 3.

Haka nan dai, ƙauye ne wanda babban madogarar kuɗin shigar mutanen cikin sa shi ne sayar da kayan marmari sakamakon albarkar ƴaƴan itatuwa da su ke da shi nau’uka daban-daban. Sai kuma a baya bayan nan da ake samun masu zuwa yawon buɗe da tabbatarwa da wancan jita-jitar azumin awa uku ɗin.

Sannan wani abu da ya kamata mutane su sani a nan shi ne, a kaf faɗin ƙasar Oman, ƙauyen WEKAN ne kaɗai garin da ke tsakiyar manyan tsaunukan da in ban da Ƙasar Saudiyya, a kaf gabas ta tsakiya, babu in da ya kai yankin da ƙauyen ya ke dogayen tsaunuka. Wannan ya sa, idan rana ta hudo daga gabas da sanyin safiya, sai kimanin wajen ƙarfe 11 na safen sannan mutanen garin ke ganin ranar. Saboda tare ta da waɗannan tsaunukan ke yi.

Kuma duk in da ƙarfe 2 zuwa 2:30pm ta yi, daga nan ranar ta ke ɓace musu da gani sakamakon kwantawa da ta ke yi zuwa ɓangaren yamma wanda nan ma dai tsaunin ne ke tare ta ba wai don ta faɗi ba ne a ɗaukacin ƙasar Oman ɗin ba.

Kenan mutanen ƙauyen Wekan, na ganin rana ƙuru-ƙuru ne na iya tsawon awanni uku zuwa da rabi ne a in da su ke, sakamakon ƙawanya da tsaunuka su ka yi musu ba wai don hudowa da faɗuwar ta ne na awa uku da rabi ɗin ba.

Don haka ɓacewar da rana ke yi musu, ba duhun dare ne ke wanzuwa ta yadda ba za ka iya ganin hatta gaban ka idan babu hasken fitila ba.

Kamar yadda Ma’aikatar Yawon Buɗe Ido na Ƙasar Oman su ka taɓa faɗa a shekarar 2016 lokacin da jita-jitar ta faro cewa: “Wannan zance ba gaskiya ba ne. Ko da ganin rana ya na da wahala a wasu wurare masu tsaunuka, hakan ba ya na nufin cewa rana ba ta fitowa ba ne gaba ɗaya”.

Ƙasar Oman wacce ke yankin gabashin duniya, ta na da iyaka da ƙasashen irin Saudi Arabia da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Yemen ta kan tudu. Sannan ta na da iyakar kan ruwa da Iran da kuma Pakistan.

Kuma duk da Ƙasar na daga cikin ƙasashen duniya da ke da ƙarancin awannin yini, in da awannin dare su ka fi na rana yawa, amma hakan ba ya nufin akwai wani yanki a faɗin ƙasar da rana ke kasancewa a iya tsawon awanni 3 ba ne. Sai dai madadin hakan, akwai lokutan da sauyin yanayi ke sakawa a yi har tsawon awanni 15 ma ana Azumi kamin a sha ruwa a Ƙasar ta Oman. Ko a yanzu haka ma (a shekarar 2022)ana yin Sahur a babban birnin Muscat na Oman ƙarfe 4:32am sannan a sha ruwa 6:25pm.

Don haka zancen azumin awanni 3 da ake yi a wannan ƙauyen ba gaskiya ba ne. Zance ne kawai na ƴan Soshiyal Midiyar da ya samo asali da tushe daga can ƙasashen Larabawa, ya keto zuwa Turai, ya gangaro zuwa nan Afirika da Najeriyar Arewa, wadda aka daɗe da jana’izar wannan shifcin gizon a ƙasashen da labarin ya faro, amma ake ta ci gaba da cin kasuwar labarin cikin harshen Hausa kusan duk shekara a shafukan Sada Zumunta na zamani.

Daga – Ahmad Nagudu

One Comment

Back to top button
error: Content is protected !!