E News

Ga Inda Asalin Sunan “RABAKAYA” Ya Fito Ba Inda Mutane Ke Tunanin Ba

Ga Inda Asalin Sunan Ya Fito, Amma Wasu Suka Sauya Shi Da Wata Manufa

Allah ne kadai zai yiwa wannan budurwa sakayya da hisabi tsakanin ta da wayanda suka mata mummunar zato wajen chanza ma’anar fassaran wannan suna data rubuta a bayan rigan ta *RABAKAYA*

Rabakaya

*RABAKAYA* Ba kalmar eskanci bane kamar yanda mutane suke tunani suke ta yada hoton wannan baiwar Allah suna daukar alhakin ta

*RABAKAYA* babban family ne a Jigawa wanda suna da nasaba da Masarautar Hadejia kuma wannan suna family name dinsu ne kamar yanda kowa suke da nasu family name din su

Na tabbata duk eskancin yarinya ba zata taba rubuta wannan sunan a bayan rigan ta da niyyar eskanci ba saboda tasan dole wannan hoton zai zagaye duniya daka karshe har iyayen ta su gani

Kamar yanda aka canza fassaran kalmar kunu haka aka canzawa wannan budurwa ma’anar sunan data rubuta, duk wanda yasan ya mata mummunan fassara yayi gaggawa ya neme ta domin yafiya. Muna mata fatan alkairi mu kuma Allah ya shirya mu da ita baki daya.

Daga Aliyu Naziru Officer

Back to top button
error: Content is protected !!