Labarai

El-Rufai Ya Sa hannu Kan Dokar Yima Masu Fyade Dandaƙa

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya rattaba hannu kan dokar hukunci mai tsanani a kan duk wanda a ka kama da laifin fyade.

 

Dokar ta ba da damar kisa ko yin dandaka ga duk wanda a ka kama ya yi wa kananan yara ‘yan kasa da shekaru sha hudu fyade.

Hakama karkashin dokar za a iya yanke musu hukuncin daurin rai-da-rai.

 

Idan a ka kama mace kuwa dokar ta ce za a cire mata wani sashe na al’aura da ake kira Fallopian tube ko kuma a kashe ta.

Nasir el-Rufai ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa tabbas ya rattaba wa dokar hannu.

A makon da ya gabata ne majalisar jihar Kaduna ta amince da kudurin dokar.

Bugu da kari duk baligin da a ka kama da laifin yiwa ‘yan kasa da shekara 14 fyade, za a saka sunan shi kundin rajistar wadanda suka aikata fyade tare da wallafa su a kafafen yada labarai.

Kawo yanzu jihar Kaduna ce kawai a Najeriya da ta tanadi hukunci mai tsanani kan masu aikata fyade a Najeriya.

A na samun koke sosai kan fyade a watannin nan a Najeriya a yan watannin nan.

Kuma duk da hukumomi na samun nasarar kama masu aikata fyaden, ba kasafai a ke yanke musu hukunci ba.

@BBCHausa

Back to top button
error: Content is protected !!