Duk Wata Malama Mace Da Take Bàtsa Da Sunan Wa’azi
Duk Wata Malama Mace Da Take Bàtsa Da Sunan Wa’azi Ba Ta Da Banbanci Da Muneera Abdulsalam A Waje Na – Dr. Sheriff Almuhajir

Wata sabuwar Malamar ta sake zuhuri, amma ni abunda ke bani mamaki, su wadannan Malaman waazin da ya fi musu dadi shine labarin aure da jíma’i, tamkar duk ayoyin Qurani akan Jimái aka sauko da su.
Tayaya za’a yi kana zaune kana kalllon kyakkaywar mace tana bayanin jima’i wani abu bai zo maka a zuciya ba?
Bayyanar Malamai mata abune mai kyau, amma baiwa wadannan matan damar hawa mimbari suna wa’azi ana sakawa a social media da sunan addinin Musulumci ban san ina aka samo shi ba.
Kuma wallahi hakan ba daidai ba ne, Domin bidah ce karara da aka kawo cikin addini, mace ta tashi daga wani gari ta hau jirgi ko mota don ta je wani gari wa’azi yaushe aka yi hakan, waye yace ayi ina hujja?







