Labarai

Duk wanda Ya Zarge Ni Akan Zuwana taron Malaman Duniya Na Iran Munafiki Ne

Duk wanda Ya Zarge Ni Akan Zuwana taron Malaman Duniya Na Iran Munafiki Ne – Dr Ahmad Mahmud Gumi

Fitaccen Malamin Addinin Musulunci a Nijeriya Dr. Ahmad Gumi Ya ce “Inda yau naga kuna fitowa kuna fada Akan Laifuffukan da Saudiyya Suke aikatawa, toh zan saurare ka Amman baka faɗin Laifuffukan Saudiyya sai Laifuffukan wanda suke so a taimakawa bayin Allah na Gaza ? Toh bazan Saurare ka ba.

Ya ƙara da cewa; Idan Lokacin da Saudiyya Suke Gayyatar mawaƙan ana Rawa da wasannin kwallo A lokacin da Ake Kashe bayin Allah A Gaza bakwa iya fitowa kuna faɗin Laifuffukan da Saudiyya suke aikatawa.

Bugu Da Ƙari Babba malamin ya ci gaba da cewa; Sai don An Gayyace Ni taron malamai Na Duniya yadda za’a Hada kan Al’ummar Musulmi, Domin Taimakon Palastine Shine zaku ga Laifin Iran?

Baku ga laifin Saudi Arabia ba? Yau idan Riyyad idan Suka tuba Suka yi kira irin wanda Iran Sukayi a shirye nake naje. Duk wanda yazo da aikin Alheri Ka taimake shi da aikin Alherin kabar masa Aqidar Sa.”

Dr Ahmad Gumin Sheikh Zazzaki

Yau ko Krista na kagani anyi Hatsarin mota a hanya suka ce maka Don Allah ka taimake su da mai (Fuel) Domin daukan mutane a kaisu Asibiti ka taimaka musu da wannan aikin Alherin. A ko da yaushe ka tsaya a tsakiya kan Fadin gaskiya da aikin Alheri.

Back to top button
error: Content is protected !!