E News

DJ AB, Ya Samu Digiri Daga Jami’ar Ahmadu Bello Zaria

SHAHARARREN mawaƙin gambara (hip-hop), Haruna Abdullahi, wanda aka fi sani da DJ AB, ya samu digiri daga Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya.

DJ AB ya kammala karatun sa a wannan shekara, inda ya karanci ‘Quantity Surveying’.

AB ya yi wa Allah godiya a soshiyal midiya tare da saka hotunan sa sanye da kayan yaye ɗalibai, inda ya ce, “Alhamdulillah! Better late than never. Bsc Quantity Surveying- ABU Zaria.”

A ranar Asabar, 27 ga Janairu, 2024 jami’ar ta yi bikin yaye ɗaliban ta a karo na 43, wanda AB ya na cikin su

AB ya shahara a harkar waƙoƙin hip-hop a arewacin Nijeriya, har ma za a iya cewa ya na kan gaba a wannan ɓangaren.

DJ AB ɗa ne ga tsohon Shugaban Ƙungiyar Furodusoshi ta Jihar Kaduna, wato Alhaji Abdullahi Sa’id Bello, mai kamfanin MDC Production da ke Kabala Costain, Kaduna.

Ɗimbin ‘yan fim da mawaƙa sun taya shi murna, ciki har da shahararren jarumi kuma Shugaban Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya (NFC), wato Ali Nuhu.

 

Back to top button
error: Content is protected !!