Kannywood

Diyar Jaruma Hadiza Kabara Tayi Saukar Alƙur’ani

Sadiya Diyar Jarumar KannyWood Hadiza Kabara Ta Yi Saukar Alƙur’ani Maigirma.

CIKIN yardar Allah da falalar sa da ya ke yi ga bayin sa, ita ma Sadiya Yakubu Gwamna, ɗiyar jaruma a Kannywood Hadiza Mohammed Kabara ta samu baiwar saukar Alƙur’ani mai girma.

A ranar Lahadi da ta gabata ne dai Hadiza ta shirya taro na musamman a gidan su da ke unguwar Panshekara a cikin garin Kano domin murnar saukar Alƙur’anin.

Taron ya samu halartar jaruman fim da dama da su ka je wajen domin taya ta murna.

Sun haɗa da Sadiya Muhammad Gyale, Asma’u Sani, Hadizan Saima, Raihan Imam Ahmad Ƙamshi, da sauran su.

Daga Shafin Fimmagazine.com

Back to top button
error: Content is protected !!