Kannywood

Darussa Kan Illar Shan Giya Da Su Ka Bayyana A Shirin Labarina

Darussa Kan Illar Shan Giya Da Su Ka Bayyana A Shirin Labarina Series

Giya haramun ce, kuma babu ta yadda za ta samar wa duk wani musulmi maganin damuwar da ya tsinci kan shi a ciki. An nuna Al-Amin a matsayin mashayin Giya ne don tura muhimmin sako da nusar da al’umma illolin ta ga duk wadda ya rungume ta a matsayin hanyar samun waraka daga damuwa. Wadda kuma babu ta yadda za a isar da wannan sakon ba tare da a aikace ba. (Nuna ana shan ta)

Daga darussan da su ka bayyana a cikin shirin kan illar shan Giya sun hada da:

– Faruk ya shaidawa Al-Amin cewa, babu wani sauki ko canji da rayuwar sa ta samu game da damuwar da ya ke ciki dalilin shan Giyar da ya fara sai ma kara samun koma baya da dulmiya cikin tashin hankali

– Tasirin illar abokin banza ya taimaka wajen bayar da shawara da tunzura Al-Amin wajen fara shan Giya a matsayin mafita yayin da ake cikin matsala

– Charity ta yi amfani da halin maye da ubangidanta ya ke ciki wajen gayyato Nadiya don su cutar da shi kamar yadda ta furta cewar kullum a cikin maye ya ke

– Faruk ya tabbatar wa maigidan sa Al-Amin hatta Sallahr da ya ke yi Allah ba ya karba dalilin Giyar da ya ke sha

– Muhammad Hassan, abokin Al-Amin ya bayyana masa cewa Allah Ya tsinewa duk mai shan Giya

– Malam Kabiru ya furta karara cewa, masifar da Al-Amin ya ke ciki na shan Giyar ya fi tashin hankalin rasa iyalan na shi ma da ya yi.

– Ma’aikatan kamfanin Al-Amin Mainasara su na ta shirya cuta da sace masa dukiya

Wannan wani bangare ne na bayanan da Yakubu M. Kumo ya yi a yayin hirar mu da shi ta cikin shirin ‘Filin Fina-finan Hausa’ na Freedom Radio Nigeria – 99.5 Kano a ranar Lahadi, 28 ga watan Janairun 2024.

Daga – Ahmad Nagudu

 

Back to top button
error: Content is protected !!