Kannywood

Dandalin Kannywood: Ni mijin ta ce ne, sai abinda matata ta ce nake yi – Cewar Ado Gwanja

A hirar da aka yi da fitaccen jarumin wasan Hausa kuma mawaki a masana’antar Kannywood Ado Gwanja

– An yi masa tambayoyi muhimmai wadanda suka shafi rayuwar shi, inda ya samu damar amsa da yawa daga cikinsu

– Jarumin ya bayyana cewa mahaifinsa ne mai shayin Sarkin Kano

A wata tattaunawa da yayi da BBC, fitaccen jarumi kuma mawaki a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Ado Gwanja yayi bayani dalla-dalla akan abubuwan da suka shafi rayuwarshi.

A lokacin da yake amsa tambayoyin manema labaran, Ado Gwanja ya amsa tambayar da aka yi masa akan karin aure, inda ya ce: “Gaskiya zai yi wuya ya sake aure, saboda basu yi haka da matarshi ba, kuma shi sai abinda ta ce yake yi,” ma’ana dai shi mijin ta ce ne.

Haka kuma da aka tambayeshi irin kalar matar da yake so sai ya ce: “Wacca na aura, amma kuma ina son mace wacce ba doguwa ba, ba gajeriya ba, sannan kuma ba siririya ba, ba kuma mai kiba ba.”

Da aka yi masa tambaya kuma dangane da sana’ar gidansu, jarumin ya bayyana cewa: “Ba dan yanzu na zama mawaki ba da tuni watakila ina can ina sayar da shayi, saboda sana’ar mahaifina sayar da shayi ce, ita na gada.”

Haka kuma mawakin ya cigaba da cewa mahaifinsu shine mai shayin Sarkin Kano, ya ce sau tari an sha aikensu su kai shayi gidan Sarki ko kuma a turo wani yazo gidansu ya karbi shayi a kaiwa Sarki.

Back to top button
error: Content is protected !!