LabaraiUngategored

Dan Majalisar Tarayya A Jihar Kano Ya Gwangwaje Kiristoci Da Kayan Kirsimeti

Dan Majalisar Tarayya A Jihar Kano Ya Gwangwaje Kiristoci Da Kayan Kirsimeti

Daga Anas Saminu Ja’en

A cikin makon da ya wuce ne zaɓaɓɓan dan majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano Hon. Lawan Abdullahi Kenken, ya gwangwaje ƙungiyar kiristocin wanda suke da mazauni a Ja’en Unguwar Lalle mazabar Dorayi.

Yayin kai wannan kyauta dan majalisar ya samu wakilcin shugaban jam’iyyar na ƙaramar hukuma Mallam Umar Yusuf Umar Kashekwabo, Inda ya mikawa kiristocin Buhunan Shinkafa 5 da ƙatoton bajimin Sa domin su bikin kirsimeti cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, su dai waɗannan kiristoci sun kasance ƴaƴan jam’iyyar APC wanda da irin gudummuwar da suka bayar ne har dan majalisar yakai gaci.
Kuma ko da a babbar Sallah data gabata sai da shi Hon.

Kenken ɗin ya yiwa al’ummar Musulmin Gwale ƴan jam’iyya da ba ƴan jam’iyya ba goma ta arziki a mazaɓu 10 da suke da su inda ya yi rabon Shanu da Raguna babu adadi Shinkafa, Lokacin kai kayan Kwashekwabo ya samu rakiyar kansilan wannan yanki Hon. Jibrin Mu’azu da sauran shugabanni da ƴaƴan jam’iyyar APC.

Back to top button
error: Content is protected !!