Labarai

Dalilin watsa bidiyon ’ya ta Hanan cikin Jirgin Shugaban Kasa A Shafin Facebook – Aisha Buhari

Uwargidan Shugaba Muhammadu Buhari, Aisha Buhari, ta kare watsa bidiyon ’yar ta Hanan da ta yi a shafin Facebook, a cikin jirgin Shugaban Kasa.

Ta ce ba ta yi ba ne don yin galatsi, tsiwa ko gwasale ’yan Najeriya ba.


Aisha, wadda ita ce mahaifiyar Hanan, ta ce ta yi hakan ne domin kara wa ’yar ta Hanan kwarin guiwa, ganin cewa sukar da aka rika yi mata ta fara damun ta.
Aisha ta watsa bidiyon ne a daidai lokacin da mafi yawan ‘yan Najeriya ke cike da haushin yadda Hanan ta dauki jirgin Shugaban Kasa aka kai ta Bauchi.
Bidiyon da Aisha ta watsa na minti 55, inda aka nuna Hanan ta na halarta wasu wurare a Bauchi.
Hanan dai ta je rangadin Masarautar Bauchi ce a ranar Alhamis a cikin jirgin Shugaban Kasa.


Rangadin na ta na da nasaba da aikin Kundin Digiri na 2, wato Masters da ta ke yi a wata jami’ar kasar waje.
Hakan ya janyo ce-ce-ku-ce a ciki da wajen Najeriya, inda Kakakin Yada Labarai na Aisha, mai suna Abdullahi Aliyu ya bayyana cewa an watsa bidiyon ne don kawai a bayyana wa mutane abin da Hanan din ta je yi a Bauchi.


Da ya ke magana da PREMIUM TIMES ta wayar tarho, Aliyu a ce mahaifiyar Hanan ta watsa bidiyon ne kawai don ta kara wa ’yar ta kwarin guiwa.


Ina tabbatar maka cewa “uwargidan shugaban kasa ba ta watsa bidiyon don kawai ta yi wa ‘yan Najeriya galatsi, tsiwa ko gwasale su ba.”


Daga nan sai ya tuna wa ‘yan Najeriya cewa uwargidan shugaban kasa kuma ya san jirgin kamfanin British Airways, ya san cewa idan za ta yi tafiya ta kashin kanta, to jirgin haya ta ke shiga.”


Ya ce iyalan shugaban kasa kan shiga jirgin shugaban kasa ne a nan Najeriya kawai idan za su yi wata tafiya a cikin kasa, don kada shigar sun jirgi ya haifar da kuntatawa ga wasu da dama, saboda dalilai a tsaro.


Sai dai kuma duk da wannan, hakan bai hana a ci gaba da ragargazar Aisha Buhari ba da kuma ‘yar ta Hanan.


Jama’a da dama sun yi wa iyalan na Buhari raga-raga a shafin Facebook, bayan tura bidiyon.
Sai dai kuma a ranar Litinin Kungiyar Kare ’Yancin Musulmi a Najeriya (MURIC) ta nuna goyon bayan ta 100 bisa 100 ga abin da Hanan ta yi.


Haka dai Shugaban MURIC Ishaq Akinbola ya bayyana ranar Litinin.

Back to top button
error: Content is protected !!