Labarai

Dalilin Daina Haska Shirin Labarina A Tashar Arewa24

Dalilin Daina Haska Shirin Labarina A Tashar Arewa24

Saira Movies Labarina Series

Sakamakon yawan tambayar da ma’abota kallon mu ke yi kan dalilin daina haska shirin Labarina Series a tashar Arewa24 kamar yadda aka saba, ga takaitaccen bayani kan dalilin don mutane su fahimci in da aka dosa:

Misali, kamar mutum ne ke kai markade ko sayen ruwan sanyi a wajen wasu da kudin sa, sai kuma ka sayi na ka Injin markaden ko kuma Firinjin, zai yi yu kuma sai ka ci-gaba da kai markaden ka na biyan kudin, bayan ka mallaki na ka Injin ko Fridge ɗin? Hakan zai yi yu? To, idan amsar a’a ce, kenan yanzu sai dai kai ma ka yi ƙoƙarin nemo waɗanda za ka dinga yi wa Markaden ko masu neman ruwan sanyi ka dinga sayar musu kenan, ko? Kamar dai da haka duniya ta ke ci-gaba, wasu ma su samu damarmaki da ƙara faɗaɗa kasuwanci da taka rawa a wani fagen. Ko?

Don haka ba faɗa ko rigima mu ka yi da Arewa24 ba kamar yadda wasu ke tunani tare da yadawa.

Sannan Alhamdulillahi, ba alfahari ba, ba tashar Arewa24 ke sayar da hajar shirin Labarina ba, a’a, idan za ku lura da kyau, shirin Labarina Project ɗin ne ke sayar da kan shi bisa ga labarin da salon sa da kuma technicalities ɗin ma. Wadda kuma hakan ya na da alaka da karɓar shirin da KU masu kallo ku ka yi ne. Domin goyon bayan ku da bibiya da gamsuwar da ku ke nunawa ne ya ɗaga shirin ba wani dalili ba ko saboda wata kafa ba. To, kenan ashe duk in da aka mayar da nuna shirin, Soyayyar da ku ke nunawa shirin zai sa ku bi shirin zuwa ko ina ne don samun gamsuwar ku. Ba wai kuma alfahari mu ke yi ba da hakan ba.

Idan ba ku manta ba, da farko, ai Season 1 da Season 2 a iya tashar Arewa24 ɗin ai kaɗai mu ke haska shirin. Amma saboda faɗaɗa kasuwancin da kuma maslahar ƙara kusanto da shirin gare ku don ku sama damar sake ganin shi a kowane lokaci, sai mu ka fara saka shi a tashar mu ta YouTube, wadda wannan ya sa aka daina maimaita shi a Arewa24 ɗin tun daga Season 3. Duk mai son sake kallon shirin sai ya tafi YouTube a kowane lokaci ya ke so.

Kasuwanci ake yi, ita kuwa kasuwa ana yin ta don riba ne. Biyan Arewa24 ake yi kuɗi su ke saka mana shirin ba wai sayar musu ©️ mu ke yi ba. Kuma kuɗaɗe masu nauyi mu ke biyan su, su ke haska mana shirin. To, tun da mun samar da ta mu tashar irin Arewa24 ɗin a kaj Tauraron Ɗan’Adam (Satellite 📡) mu ma, mene ne laifi don mun dakatar da biyan kuɗi tun da mu na da ta mu?

Sannan fa a in da ake kama Arewa24 ɗin nan, anan za a samu Saira Movies TV ɗin ita ma. Duka su na kan Satellite TV ne. Kuma mu ta mu Free-to-air Broadcasting ne ma. Kyauta ba wai biya ake yi ba.

Idan ba mu yi haka ba, ta ya ya za mu raya ta mu sabuwar tashar da mu ka kafa ɗin har ita ma ta taka rawar ta a fagen?

Ayi searching 🔎 kawai a Nilesat ko Eutelsat ko Amos 17 za a samu tashar Saira Movies TV in sha Allah.

Wannan kawai shine gaskiyar lamari kan wannan lamari.

Mun gode da bibiya da shawarwari da haƙurin kasancewa da mu a kowane lokaci.

— Ahmad Nagudu
Media Promoter/Aide
Saira Movies Investment Limited

Back to top button
error: Content is protected !!