Kannywood

Dalilin Da Yasa Na Shirya Fim Din Ummi Sambo – Rukayya Dawayya

Duk A Cikin Shirin ‘Yan Fin da Finafinai, Wanda Jaridar Dimokuraɗiyya ke ɗaukar nauyi
Wakilinmu Mukhtar Yakubu Kano
A daidai lokacin da ake ganin harkar fim ta shiga wani hali na rashin tabbas dangane da harkar kasuwanci, sai ga shi tsohuwar jaruma Rukayya Dawayya, ta shirya wani gagarumin fim wanda aka kashe masa miliyoyin kudi a wajen aikin sa.

Wannan ya sa mutane su ke yin mamakin yadda Rukayya Dawayya ta kashe wannan makudan kudade domin shirya wannan sabon fim din mai suna Ummi Sambo.

Don kuwa ba don an san Dawayya ta shafe tsawon shekaru ta na shirya manyan finafinai da su ke cin kudi ba, da sai a ce kudin wani ne ba na ta ba, amma da ya ke ba sabuwar hannu ba ce, babu abin da za a ce sai dai a jinjina mata.

Ganin yadda ake ta yawan magana a kan fim din mun ji ta bakin Rukayya Dawayya dangane da dalilin ta na yin fim din kuma me fim din ma ya kunsa?

Farko ta fara ne da cewa “To duk masu fadar magana a kan fim din Ummi Sambo, zan iya cewa abu ne da ya zo musu a ba zata, saboda ina ganin ba su san ko wacece Rukayya Dawayya ba.

Domin ga duk wanda ya sanni, to na dade ina yin fim, tun a shekarun baya, kuma Idan na tashi yin fim din ina kashe kudi mai yawa domin a samar da abin da ake bukata wajen isar da sako, don haka wannan fim din sabo ne amma aiki irin wannan ba sabo ba ne a Kamfanin Dawayya.

Ko wanne irin labari fim din ya ke dauke da shi?

Sai ta ce “To labari ne na yadda mata idan za su yi aure idon su ya ke rufewa, kawai saboda sun matsu su yi auren, don haka daga mutum ya zo wajen su, sai kawai su ce ya fito a yi aure, to irin wannan yanayi ya na jefa mata cikin garari musamman a wannan lokacin, sai ka ga an yi auren, daga mace ta tare sai ta ga mijin ya zo mata da wata siffa ta daban, karshe ba a je ko’ina ba sai auren ya mutu, kuma sai a rinka zargin matan cewa sun ki zaman aure, irin abin da ya ke faruwa kenan a yanzu, musamman ma ‘yan fim, don haka na yi fim a kan wannan matsalar.

Ko kina ganin za ki mayar da kudin da kika kashe ganin cewar kin zuba kudi masu yawa a wajen aikin fim din?
Sai ta ce ‘To manufar fim din dai isar da sakon da ya ke ciki shi ne a gaba, mu a harkar fim sai dai godiya ga Allah, domin harkar ita ce ta yi mana riga ta yi mana sutura, don haka babu abin da mu ka rasa a harkar, muna sa ran mu ci kasuwar da kudin mu zai dawo har ma mu ci riba, amma dai isar da sokon shi ne a gaba na”.

Daga karshe Rukayya Dawayya ta yi Kira ga jama’a masoya da su taya ta da addu’a domin samun nasara dangane da fitowar fim din,
Ana sa ran tuni aka fara haska fim din Ummi Sambo a Sinima da ke Ado Bayero Mall wato Shooprite dake Kano daga ranar Juma’a 6 ga wannan watan na Disambar nan da muke ciku kuma za a shafe tsawon sati guda ana haskawa.

Back to top button
error: Content is protected !!