Kannywood
Dalilin Da Yasa Na Rungumi Mace A Fim
Adam A, Zango Yayi Bayanin Dalilin Da Yasa Ya Rungume Mace A Cikin Shirin Fim Din Asin Da Asin. Anga Jarumi Adamu A, Zango Ya Rungumi Amira Lokacin Data Fadi Bakinta na Zubda Jini, Inda Adamu Ya Taho Da Gudu Tare Da Rungumarta Yana Kiran Doctor, Duk A Cikin Shirin Na Asin Da Asin.
Wannan Wajen Ya Cika Mutane Da Mamaki, Inda Mutane Su Fara Cece Ku Ce, Kan Cewa Taya Za.ayi Ya Rungumeta Alhali Ba Muharraminsa Ba, Wasu Ma Cewa Sukeyi Hausa Film Har Sunyi Lalacewar Haka.
Kowa Dai Da Abin Da Yake Cewa, Sai Dai Jarumin Ya Fito Ya Wanke Kansa Tass, Game Da Wannan Lamarin, Inda Yama Mutane Cikakken Bayanin Yadda Lamarin Ya Faru Da Kuma Yadda Aka Shirya Abun.