Dalilin Da Yasa Na Hakura Da Harkar Hausa Fim – Rashido Labbo
Tsohuwar jarumar Kannywood mai suna Rashida Lobbo ta ce aure tayi shiyasa ba a ganinta a fina-finaik. Tayi Bayanin Da Yasa Ta Hakura Da Harkar Hausa Fim Gaba Daya
Kamar yadda ta bayyana, tana zaune ne a kasar Thailand a cikin birnin Bangkok tare da mijinta dan asalin kasar Mali
– Jarumar tace ta boye aurenta ne don wannan rayuwarta kadai ta shafa
Tsohuwar jarumar fina-finan Hausa mai suna Rashida Lobbo ta zanta da fim magazine bayan da tayi shekara daya ba a ji duriyarta ba a masana’antar.
Amma kuma bayan rashin ganinta, Rashida na wallafa hotunanta a shafukanta na sada zumuntar zamani a kasar Thailand.
Kamar yadda tsohuwar jarumar ta bayyana, ita haifaffar kasar Kamaru ce kuma tayi karatu a Najeriya inda ta zauna da ‘yan uwanta a Abuja. Rashin cikar burinta na zama ma’aikaciyar gidan talabijin yasa ta fada harkar fim. Tayi fina-finan Hausa da na turanci a masana’antar Nollywood.
A zantawar da aka yi da Rashida, ta bayyana cewa tayi aurene kuma suna zama tare da mijinta mai suna Abubakar dan asalin kasar Mali, a birnin Bangkok dake Thailand.
Jarumar tace sana’ar mijinta siyar da gwal kuma yayi shekaru 26 a kasar Thailand.
Ta bayyana cewa tana matukar kewar abokan aikinta na masana’antar fim kuma tana kewar mahaifiyarta don tun a 2018 da tayi aure bata sake zuwa Najeriya ba.
Da aka tambayeta dalilin da yasa ta bar masana’antar kuma tayi aure a sirrance, jarumar ta ce saboda lamarin rayuwarta kadai ya shafa. Tana jin harshen faransanci ne saboda mahaifiyarta na kasar Kamaru kuma tana zuwa hutu. Harshen turanci kuwa tana jinshi ne saboda karatun da tayi a Najeriya.
Ta bukaci addu’a daga masoyanta tare da fatan zaman lafiya da zuri’a ta gari, don har yanzu bata haihu ba.