Kannywood

Dalilin Da Ya Sa Ban Dulmuya Kai Na A Harkar Siyasa Ba – Nafisa Abdullahi

Fitacciya Jarumar masana’antar shirya-shirya fina finan Hausa Nafisa Abdullahi Sai wata Rana ta bayyana dalilin daya saka bata dulmuya hannun ta a cikin harkar siyasa ba.

Jaruma Sai wata Rana, tace tana da masoya da dama a fadin kasar nan wadanda suke harkar siyasa, babu dadi ta fito karara ta bayyanawa duniya ga Wanda take goyon baya a fagen siyasa.
Magoya bayan ta da dama zasu iya bin raayin ta wajen zaben Dan siyasa saboda irin son da suke yi mata, to amma ta kyautata musu kenan?
Tace ta fiso dukkan masoyan ta kowa ya zabi Wanda yake so daga ko wace irin Jam’iyya, kamar yadda ta bayyana a lokacin da take tattaunawa da manema labarai.
Tace ita ma tana da Wanda take so kuma shi ta zaba, sai dai baza ta bayyanawa duniya Wanda ta zaba ba; inji ta
Back to top button
error: Content is protected !!