Dalilan Dasu Sanya Abba Kabir Yusuf Nasara A Kotun Koli
Dalilan Dasu Sanya Abba Kabir Yusuf Nasara A Kotun Koli.
Kotun ƙolin Najeriya ta tabbatar da nasarar da Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ya samu a zaɓen gwamnan jihar Kano na shekara ta 2023.
Mai shari’a John Okoro wanda ya karanta hukuncin ya ce kotun ɗaukaka ƙara ta yi kuskure wajen tabbatar da hukuncin kotun sauraron ƙorafin zaɓen jihar, wadda ta ce Abba Kabir bai samu rinjayen ƙuri’u a zaɓen ba.
Saboda haka nan kotun ta yi kuskure wajen zabtare wa Abba da NNPP ƙuri’u.
A game da batun rashin kasancewar Abba Kabir ɗan jam’iyyar NNPP, kotun ta ce jam’iyya ce kawai take da ikon tantance wanda ɗanta ne ko kuma a’a.
Saboda haka ne kotun ta amince da ɗaukaka ƙarar jam’iyyar NNPP tare da yin watsi da hukunce-hukuncen kotun ɗaukaka ƙara da kuma ta sauraron ƙorafin zaɓen jihar.
Wannan shi ne mataki na ƙarshe a turka-turkar da aka kwashe watanni ana yi game da sahihancin sakamakon zaɓen na gwamnan jihar Kano.
Tun da farko, kotun zaɓen gwamnan Kano a watan Satumban 2023 ce ta soke ƙuri’a 165,633 wadda in ji ta, aka yi wa ɗan takarar na jam’iyyar NNPP aringizo, bayan hukumar zaɓe a watan Maris, ta ce ya samu ƙuri’a 1,019, 602.
Gwamna Abba dai bai gamsu da hukuncin ba, don haka ya wuce zuwa kotun ɗaukaka ƙara.
Sai dai, ita ma kotun ɗaukaka ƙarar ta bai wa jam’iyyar APC nasara bisa hujjar cewa Abba ba ɗan jam’iyyar NNPP ba ne lokacin da aka tsayar da shi takara, don haka ta nemi a rantsar da ɗan takararta Nasiru Gawuna.
A ranar 20 ga watan Maris na 2023 ne Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC ta ayyana Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan na jihar Kano.
Babban jami’in tattara sakamakon zaɓen gwamnan, Farfesa Ahmad Doko Ibrahim ya bayyana cewa Abba Kabir ya samu ƙuri’u 1,019,602, yayin da Nasiru Gawuna ya samu ƙuri’u 890,705.
Hujjojin da kotun ta dogara da su
Mai shari’a John Okoro wanda ya karanta hukuncin, ya ce an yi shari’ar ne a kan zargin jabun katin zama ɗan jam’iyyar NNPP da Gwamna Abba Kabir ya yi, da kuma aringizon ƙuri’u da INEC ta yi wa Abba.
Mai shari’a Okoro ya ce ɗaya daga cikin manyan batutuwan shi ne ko kotun ƙasa ta yi daidai wajen soke ƙuri’un Gwamna Yusuf guda 165,616.
Har ila yau, mai shari’ar ya ce ya lura da tambayar ko kotun ta yi daidai wajen yanke hukunci a kan batun zaman Abba ɗan takarar gwamna na NNPP.
“Na gano cewa matakin kotun sauraron ƙorafin zaɓe na cire ƙuri’a 165,616 daga sakamakon zaɓen Gwamnan Kano ya dogara ne kan tanadin dokar zaɓe ta 2022,” in ji J Okoro.
Sai dai mai shari’ar ya ce tanadin ba shi ne yake tantance abubuwan da ake yi a rumfunan zaɓe ba.
Ya kuma yi tambayar cewa, “Mene ne tasirin takardar kaɗa kuri’a da ba ta da alamar hukumar zaɓe?”
Ya ƙara da cewa, “Ba lallai ne a ce ƙuri’ar da ba ta da alamar INEC, ba ta da inganci ba.”
Mai shari’a Okoro ya buƙaci cewa dole ne a tabbatar cewa ƙuri’ar zaɓen, ba ita aka kai domin gudanar da zaɓen ba.
“Babu wata hujja da ke nuna cewa ba wata ƙuri’a daban aka yi amfani da ita a zaɓen ba. Don haka ya kamata a yi watsi da matakin kotun ɗaukaka ƙara na amincewa da hukuncin kotun ƙorafin zaɓe,” in ji Mai shari’a Okoro.
“A karshe, kotun sauraron korafin zaɓe ta yi kuskuren yanke hukunci kan ingancin ƙuri’un da aka kaɗa.
Don haka, an mayar wa Gwamna Yusuf duk kuri’unsa da aka soke,” in ji Okoro.
Daga BBCHausa