Labarai

Dalilan Da Susa Dala Ta Fara Karyewa A Ranar Laraba Zuwa Alhamis

Dalilan Da Susa Dala Ta Fara Karyewa A Ranar Laraba Zuwa Alhamis

Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta ɗauki matakin kai sumame da kama masu ɓoye Dala da canjin kuɗi ba bisa ƙa’ida ba a kasuwannin ƴan canji dake Abuja, Ibadan, Kano da Aba.

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa, EFCC ita ce ta kai sumamen wanda sakamakon hakan Dala ta faɗo da kaso 2.89 kimanin Naira 1,621.41, yayin da ta faɗo da kaso 0.82, kusan Naira 1,840 a kasuwar ƴan canji.

A sumamen da jami’an hukumar ta EFCC suka kai Abuja sun yi nasarar kama kimanin mutum 10 waɗanda ake zargi da kasuwancin ba bisa ƙa’ida ba. Wanda kuma bayan yaɗuwar labarin shaguna da dama suka rufe a Legas, Abuja da Kano.

“Shugaban kasuwar ƴan canji na (WAPA) da ke Kano, Alhaji Sani Salisu Dauda ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya tabbatar da cewa hukumar (EFCC) ta kai sumame inda ta kama waɗanda suke ɓoye Dala da masu sana’ar Canji ba bisa ƙa’ida ba.

Ƙungiyar ƴan canji ta yi maraba da matakin na gwamnati na kama masu canjin kuɗi a bakin hanya, “muna goyon bayan duk wani mataki da zai taimaka wajen tsaftace harkar canji ya kawar da masu yin sana’ar a bakin hanya domin duk Duniya ba inda ake canjin kuɗaɗen ƙasar waje barkatai a bakin titi sai nan, saboda haka muna goyon bayan wannan mataki”. Cewar shugaban ƙungiyar ƴan canji, Aminu Gwadabe.

Baya da wannan matakin ma tuni gwamnati tana ƙoƙarin daƙile duk wasu shafukan yanar gizo na hada-hadar kuɗaɗe waɗanda ke ƙara ta’azzara hauhawar farashin Dalar a Najeriya.

Back to top button
error: Content is protected !!