Dalilan Da Suke Sani Fitowa A Wakokin Gidan Gala
Dalilin Da Yasa Nake Yawan Fitowa A Wakokin Gidan Gala, Tahir Facce Yayi Bayani Game Da Abin Da Yasa Yake Yawan Fitowa A Bidiyoyin Inda Ake Ganin Jarumin A gidan Gala Yana Rawa Tare Da Kananan Yan Mata Masu Karamin Shekaru.
Ire Iren Wadannan Bidiyoyin Suna Yawan Jawoma Jarumin Cece Ku Ce, Inda Da Dama Wasu Mutanen Ma Sun Daina Ganin Girman Jarumin Kamar Yadda Suke Gani A Baya, Inda Wasu Ke Cewa Bai Kamata A Dinga Fitowa Ana Ganinsa Cikin Sa’o’in Jikokinsa Ba, Yana Rawa Ba.
Inda Shi Kuma Jarumin Ya Fito Ya Kare Kansa, A Wata Hira Da Mujjallar Fim Tayi Dashi, Inda Yace Dalilinsa Da Yasa Yake Fitowa Yana Rawa A Gidan Gala Shine, Akwai Wani Lokaci Da Cutar Ciwon Suga Ya Tasoshi A Gaba, Kuma Bashi Da Kudi,
Sai Wadannan Yaran Suzo Su Sameshi Har Gida Kan Yazo, Yayi Musu Wasa A Gidan Na Galansu, Koda Kuwa Baiyi Rawa Ba Kawai Ya Zauna A Matsayinsa Na Babban Jarumi.
Ana Hakane Kuma Ya Sami Halartar Wasan, Kuma Har Yaji Daukin Jiknta Inda Har Ya Sami Damar Yin Rawa. Zuwansa Wasan Ne Cikin Ikon Allah Har Ya Sami Zunzurutun Kudi Naira Dubu Dari A Wajen Wasan.
Jarumin Yayi Bayani Mai Tsayi, Tare Da Kare Kansa,
Ku Kalla Wannan Bidiyon Domin Kuji Yadda Yayi Bayani A Tattaunawarshi Da Mujjallar Fim.








Allah yasa mu dace