E News

Dakta Maryam Shetty (QUEEN OF THE NORTH): Kowa Yaga Zabuwa

Dakta Maryam Shetty (QUEEN OF THE NORTH): Kowa Yaga Zabuwa Da Zanenta Ya Ganta

Maryam Shetty

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

Hausawa Sun Yi Gaskiya Da Su Ka Ce “Kowa Ya Ga Zabuwa, To Da Zanenta Ya Ganta”. Ma’ana, Kowa Ya Ga Dakta Maryam Shetty, To Babu Ko Shakka Da (Alherinta Ya Ganta) Mace Ce Mai Ƙoƙari Da Himma Wajen Taimakon Al’umma Da Gina Rayuwar Mata Da Matasa.

A duk inda jama’a su ka ji an ambaci sunan matashiyar ƴar Siyasa, sarauniyar Arewa, Garkuwar Matasa, Dakta Maryam Shetty, babban abin da ya ke zuwa cikin tunaninsu shi ne alkhairanta, haba-habarta da jama’a, tausayinta da jin ƙanta ga al’umma.

Mawuyacin abu ne ka je wani wurin taron jama’a a ciki da wajen Jihar Kano ka ambaci sunan Dakta Maryam Shetty ka ji wani ya faɗi sharrinta ko wani mummunan furuci na ƙiyaya ko adawa akanta. Duk inda ka je za ka ji al’umma su na yabonta da kuma saka mata albarka da fatan alkhairi a rayuwarta.

A saboda yadda Hajiya Maryam Shetty ta ke da ƙoƙarin jin ƙai da taimakon al’umma, har laƙabi ake yi mata da (Dianar Afrika). Sanin kowa ne Princess Diana wata mata ce wacce ta rayu a tsakanin shekarun (1961–1997). Kuma matar ta yi ƙaurin suna ta kuma shahara a ƙasar Birtaniya da Duniya gaba ɗaya akan ayyukan jin ƙai da taimakon yara ƙanana da al’umma gaba ɗaya.

A saboda alkhairan Diana, bayan mutuwarta Sarauniyar Ingila sai da ta aike da saƙon ta’aziyyar rasuwarta, inda a cikin jawabin jimamin rasuwar da ta gabatar a gidan talabijin, sarauniyar ta Ingila, Queen Elizabeth ta II ta bayyana cewa “babu wani mutum da ya san Diana da zai iya mantawa da ita. Miliyoyin al’ummar da ba su taba ganinta a zahiri ba, amma su na jin labarinta ba za su taɓa mantawa da ita ba. Rayuwarta abar koyi ce ga sauran al’umma”. Inji Sarauniyar Ingila.

Sannan kuma Bayan rasuwar Diana, an yi mata laƙabi da “People’s Princess”, wato ma’ana (Sarauniyar Al’umma), saboda ɗumbin ayyukan alkhairin da ta yi na taimakon al’umma wanda kuma ya game duniya gaba ɗaya a lokacin rayuwarta.

To kamar haka ne jama’a su ke kwatanta Hajiya Maryam Shetty da (Tauraruwar Matan Arewa) da (Garkuwar Matasan Arewa) a saboda yadda a kullum hasken alkhairanta ke ƙara bazuwa zuwa ko’ina a ciki da wajen Jihar Kano ta yadda hatta mutanen da ba ƴan Kano bama alkhairanta na isa gare su kuma su na yi mata godiya da yabo da fatan alkhairi kan taimako da alkhairan da ta ke yi musu.

A saboda yadda Hajiya Maryam Shetty ta kasance jarumar mace, al’umma ne su ke kwatanta ta da (Raziya Sultana) ta ƙasar Indiya. Duba da yadda su ka yi tarayya ko kamanceceniya da juna ta fuskar ba da gudunmawa da tallafawa wajen samun nasarar mulki a ƙasa.

Tarihi ya tabbatar da cewa Raziya Sultana Basarakiya ce da aka taɓa yi a birnin Delhi na ƙasar Indiya, kuma ta gudanar da mulki daga ranar 10 ga watan Octoba, 1236 zuwa 14 ga watan Octoba, 1240. Ta gaji sarauta ne daga mahaifinta mai suna Shams’uddin Iltutmish. Sannan kuma Ita ce mace ta farko da ta taɓa yin sarauta a masarautar Delhi bayan rasuwar mahaifinta.

Haka zalika, tun kafin zamanta Sarauniya, Raziya ta kasance makusanciya ta kusa da kusa ga mahaifinta akan harkokin mulki. Ta fannoni daban-daban ta tallafawa mahaifinta inda ta zamto garkuwa da kuma kariya a gare shi. Kuma mahaifinta ya nuna mata kulawa ta musamman ya ja ta ajiki matuƙa wajen taya shi tafikar da mulki. Domin kuwa ko a shekarar 1230 lokacin da mahaifinta ya tafi wani yaƙi, Raziya ce ta zauna akan matsayin mahaifin nata da taimakon wani amintaccen ministansa ta gudanar da harkokin mulki har zuwa lokacin da mahaifin nata ya dawo.

Sannan kuma bayan dawowarsa daga wannan yaƙi a shekarar 1231, Sarki Iltutmish ya nuna Radiya a matsayin wacce za ta gaje shi bayan mutuwarsa saboda ƙaunar da ya ke mata duba da yadda ta ke taimaka masa wajen ba shi kariya da neman nasarar mulkinsa da kuma irin hazaƙa da ƙoƙarin da ta nuna akan gudanar da ayyukan sarautar a lokacin da ya tafi wannan yaƙi. Haka zalika Sarki Iltutmish ya kasance sarki na farko a tarihin Delhi da ya taɓa sanya mace a matsayin wacce za ta gaje shi. Sannan kuma Raziya ta kasance mace ta farko da ta taɓa sarautar Delhi.

Irin wannan ƙwazo da hazaƙa na Sarauniya Raziya shi ne ya ke kamance da na Hajiya Hajiya Dakta Maryam Shetty har al’umma su ke yi mata kallon (Raziyar Afrika), saboda ƙoƙarinta na shiga harkokin mulki ta ba da gudunmawa a matsayinta na ƴar manya jinin sarauta.

Domin kuwa mafi yawan ƴaƴan manya musamman mata a yanzu a zaune su ke kawai su na jiran a ba su, kuma ba sa fita yaƙin neman zaɓe. Amma ita Hajiya Dakta Maryam Shetty ta fita daban domin kuwa kuɗinta ta ke fitarwa ta kashe akan harkokin siyasa. Sannan kuma ita da kanta ta ke shiga loko da saƙo a zaɓukan da su ka gabata domin nemawa jam’iyyar APC goyon bayan al’umma, kuma da wannan taimako nata an samu gagarumar nasarar da ƙila da ba ta ba da gudunmawa, sai an fuskanci matsala da ba za ta gyaru ba.

A saboda kyawawan ɗabi’u da halayenta Hajiya Maryam Shetty ta samu laƙabin suna (Ƴar Aljannah) da manufar addu’a da kyautata mata zaton samun Aljannar a ranar gobe ƙiyama. Domin mace ce wacce ba ta da ƙyashi ko hassada da nuna ƙyama ko ƙiyaya ga al’umma.

Hajiya Maryam Shetty zuciyarta a wanke ta ke fesfes a kullum burinta da fatanta shi ne ta taimaki jama’a ta gina al’umma domin cigabansu da cigaban ƙasa gaba ɗaya.

Mu na yi mata fata da Addu’ar Allah ya kare ta daga sharrin maƙiya da mahassada. Allah ya ƙara mata ƙarfin gwiwa da ɗaukaka me ɗorewa.

Back to top button
error: Content is protected !!