E News

Daga Cikin Illoli Da Guguwar Tiktok Da Ya Tafi Da Matan Zamani

Daga Cikin Illoli Da Guguwar Tiktok Da Ya Tafi Da Matan Zamanin Nan…

A Dalilin Tiktok Din, Akwai Kananan Yan Matan Da Don Neman Background Din Da Za Su Yi Recording Na Bidiyoyin Da Za Su Wallafa A Shafukan Su Su Burge,

Su Kan Bi Namiji Zuwa Dakin Hotel Su Kasance Tare Da Shi Ya Yi Duk Abun Da Ya Ke So Da Su Ba Tare Da Ya Basu Ko Sisi Ba, Don Kawai Su Samu Wannan Damar Nadar Bidiyon A Ciki Da Wajen Hotel Din Su Yi Posting Don Su Burge.

Saboda Ka Na Ganin Wuri Ko Muhallin Da Su Ke Bidiyon Ka San Ba Gidajen Iyaye Ko Na Yan Uwan Su Ba Ne, Kuma A Shekarun Su, Bai Kamata A Ce Za Su Wanzu A Wadannan Wuraren Su Kadai Ba.

Wasu Kuma Muddin Su Ka Kyalla Ido Su Ka Ga Namiji/Saurayi Gidan Su Ya Qawatu, Akan Wannan Kadai Shima Za Su Kulla Alaqa Tare Da Sakar Masa Jiki Don Kawai Su Samu Damar Wanzuwa A Haraba Da Cikin Gidan Su Idan Su Ka Ga Da Damar Hakan Don Nadar Bidiyon Wallafawa A Tiktok.

Daga – Ahmad Nagudu

Back to top button
error: Content is protected !!