Kannywood

Dadi Kashe Ni Inji Barawon Zuma : Ko Kun San Waye Halima Atete Zata Aura Kuwa ?

Dadi Kashe Ni Inji Barawon Zuma : Ko Kun San Waye Halima Atete Zata Aura Kuwa ?

Batun auren fitacciyar jaruma Halima Yusif Atete daya daga cikin manyan jarumai a masana’antar finafinai ta Kannywood ya ja hankalin masu kallon, dama bibiyarsu shafukan sun a soshiyal midiya da ma yan masana’antar ta kannywood
A yan kwanakin nan ne dai maganar auren Halima Atete ta kara yin karfi a cikin masana’antar fina-finai ta Kannywood, wanda hakan ya sa duk inda ka samu ‘yan fim sai ka ji labarin su ke yi.

Baya ga haka ma labarin ya kara karfi ne ta yadda aka ga na kusa da ita su na dora labarin a shafukan su na soshiyal midiya.

A sakamakon hakan ne ya sa Sashin labarai na Northflix ya nemi jin ta bakin jarumar Halima Atete kan gaskiyar maganar auren na ta, sai dai duk kokarin da muka yi na samun ta abin ya gagara, kuma mun yi ta kiran ta a waya ba ta daga ba, baya ga sakon kar ta kwana da muka tura mata amma ba mu samu amsa daga gare ta ba.

Sai dai daya daga cikin makusantan ta Isa Bawa Doro ya tabbatar mana da gaskiyar maganar auren, in da ya shaida mana cewar, ai an ma daga auren ne shi ne ya sa ba a yi ba, domin an shirya za a yi auren ne a cikin wannan watan na Disamba, amma sai aka daga shi zuwa sabuwar shekara.

Mun tambaye shi ko wa Halima Atete za ta aura?

Ya amsa mana da cewa; Har yanzu babu Wanda zai iya fada maka mutumin da Halima za ta aura domin kowa hasashe ya ke yi, amma a hasashen da mutane ke yi shi ne ana zaton Isiyaku ferus mawakin siyasar nan da ya yi tashe wajen wakar Buhari da Jam’iyyar A P C za ta aura.

Jarumar ta dauki lokaci mai tsawo ta na soyayya da mawakin, kuma soyayyar ta su ba a boye take ba, domin a tsawon zaman Halima Atete a harkar fim, babu wani da aka taba gani ta bayyana soyayyar sa a fili kamar ta sa, saboda haka ne ma aka fi kyautata zaton shi ne angon na Atete.

Back to top button
error: Content is protected !!