Kannywood

DA DUMI DUMIN SU:-Kotun Musulunci A Kano Zata Hukunta Rahama Sadau

Daga Barista Nuraddeen Isma’eel
Kotun Musulunci wacce take Kano, zata hukunta shahararriyar jarumar wasan kwaikwayo rahama sadau, bisa keta Haddi na Addinin Musulunci da takeyi a bainin duniya,

Majiyarmu: ta samu wannan labari daga jaridar Alfijir hausa a shafinta na facebook.

Hakan yakara budo wata fai-fai ne, na jawo! Ire-iren Shigar da takeyi masu muni, na karancin tarbiyya a idon ta, kamar ba diyar musulma ba, tana abunda ko Kirista basayi, indai a sahihin al’adar su ne na kiristancin.
Majiyar namu ta tabbatar mana da cewa” kotun na Musuluncin, tasha alwashin hukuntata, dai-dai da Abinda tayi.

Kana” rahoton namu, a Inda yaci gaba da cewa, Kotun zata kai mata sammaci, a Cikin wannan watan na disamba.

Sai dai kotun bata ayyana ko wani rana bane, na kamata sammacin, amma Kotu tayi kudurin hukuntata, kuma doka zatayi Aiki akanta ita kadai, idan kuma da umarnin iyayen ta ne, take keta haddin Addinin Musulunci Suma doka zata hukunta su kai tsaye, domin su zama darasi ga sauran jama’a.

Gare Ku masu karatu Na Ra’ayoyin mu ????

Back to top button
error: Content is protected !!