E News

Ci Gaban Kananan Sana’O’I Na Daga Cikin Ma’aunin Nasarar Gwamnatin Mu.

Ci Gaban Kananan Sana’O’I Na Daga Cikin Ma’aunin Nasarar Gwamnatin Mu. – Kashim Shetima

Kashim Shetima

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ne ya furta hakan a yayin da yake kaddamar da shalkwatar hukumar kula da masu kananan sana’o’i ta kasa(SMEDAN) a ranar 20/12/23 a Abuja.

Sanata Kashim Shettima ya kara da cewa gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba za ta taba yin kasa a gwiwa ba wajen ganin ta kare ‘yan kasuwa da kasuwancinsu a Najeriya a matsayin su na ginshikin alkiblar gwamnatin mai taken Fata Nagari da ke aiki tukuru don samar wa da milyoyij ‘yan Najeriya ayyukan yi, da samar da jari, da bunkasar tattalin arzikin da zai kawar da fatara ya sake farfado da kasar.

“Yanzu ne lokaci mafi dacewa ga bayar da kariya ga kamfanoni a Najeriya, ba kawai don suna matsayin madogarar al’umma ba, har ma da zamowarsu ‘yar manuniya ga nasarar gwamnati. Lokaci ne zai zama alkali kan irin namijin kokarin da Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ke yi don kare kasuwancinmu da yadda ya mai da hankali kacokan kan shirin farfado da tattalin arzikinmu” inji Mataimakin Shugaban kasar

Mataimakin ya kuma tunatar da cewa ya kaddamar da hukumar MSME ta kasa kwanaki goma da suka gabata, inda ya ce wannan somin tabi ne idan aka yi la’akari da abubuwan da ke tafe.

Malam Kashim Shettima Ya sake jaddada Albishir ga ‘yan kasa kan hadin gwiwar tsakanin gwamnati da Bankin masana’antu don kaddamar da bayar da bashin Naira biliyan 75, mai karancin ruwa na 9% ga kamfanonin kasuwanci a Najeriya wanda zai fara aiki a watan Janairun 2024.

*Stanley Nkwocha* *Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da sadarwa a ofishin Mataimakin Shugaban Kasa)*
*20 ga Disamba, 2023*

Back to top button
error: Content is protected !!