Kannywood

Burina Na Shine Na Zama Hamshakiyar ‘Yar Kasuwa – Rayya Kwana Casa’in

kwana casa'in
Rayya90Days Instagram

Tauraruwar fina-finan Hausa Surayya Aminu wacce aka fi sani da Rayya a cikin shirin talabijin na Kwana Casa’in na tashar Arewa24 ta ce tana da burin zama hamshakiyar ‘yar kasuwa.

Fitacciyar ‘yar wasan Hausan ta bayyana hakan ne lokacin da muka yi wata hirar musamman da ita a shafinmu na Instagram.

Kodayake ‘yar wasan ta ce an haife ta ne a jihar Legas kimanin shekara 21 da suka wuce, amma ta taso ne a jihar Kaduna.

Surayya ta ce ta shahara ne sanadiyyar fitowarta a wasan Kwana Casa’in, amma ta fara wasan Hausa ne wata shida kafin nan.

“Na yi fina-finai kamar Hanyar Arziki da Yarena da Kanin Miji da wasu da ba su fito ba tukunna,” in ji ta.

Har ila yau ta ce tun tana karama take sha’awar aikin jarida wanda yana daya daga cikin abubuwan da suka sa ta fara sha’awar shiga harkar fim.

Ali Nuhu ne jarumin da ya fi burge ta, kamar yadda ta ce kuma a bangaren mata ta fi son Rahama Sadau da Fati Muhammad.

Daga nan Surayya ta ce yanzu haka tana karatun difloma ne a bangaren aikin jarida kuma tana da burin ci gaba da karatunta zuwa matakin digiri har ma gaba da haka.

Amma ta ce a halin yanzu tana kasuwanci, inda take harkar samar da lantarki daga kimiyyar rana wato Solar.

A karshe ta ce tana da burin zama hamshakiyar ‘yar kasuwa kuma a lokaci guda fitacciyar ‘yar jarida.

 

@BBCHausa

Back to top button
error: Content is protected !!