Buhari Ya Nada Jarumin Kannywood Nura Hussaini Da wani Babban Mukami
Buhari ya nada dan Hausa fim a matsayin kwamishinan hukumar alhazan Najeriya
- Jarumi Nura Hussaini Yakasai dai an bashi mukamin kwamishin tsare-tsare da kudi na hukumar daga jihar Kano
- Inda a jiya shugaban kasar Muhammadu Buhari ya aika da jerin sunayen ga majalisar tarayyar kasar nan
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike wa majalisar dattawan tarayyar Najeriya sunayen shugabanni, Kwamishinoni da kuma Membobin da wakilan hukumar alhazan Najeriya wato (NAHCON).
Daga cikin sunayen wadan da shugaban kasan ya aike zuwa majalisar, wacce ita kuma ta karanta a jiya Talata 3 ga watan Disambar shekarar 2019 a gaban ‘yan majalisun kafin ta dage zaman zuwa yau Laraba 4 ga watan Disambar wannan shekarar.
A cikin jerin kwamishinonin dai har da shahararren dan Fim din nan na kungiyar Hausa fim ta Kannywood wato Nura Hussaini Yakasai, wanda aka bashi mukamin kwamishin tsare-tsare da kudi na hukumar daga jihar Kano.
Ga sunayen shugabannin hukumar da kwamishinoni:
- Zikrullah Olakunle Hassan ~ Chiarman (Daga jihar Osun)
- Abdullahi Magaji Hardawa~ Komshinan Sintiri (Bauchi)
- Nura Hussaini Yakasai~ Kwamishinan Kudi da tsare tsare (Kano)
- Sheikh Momoh Suleiman~
- Kwamishinan Yada Labarai da Kididdiga (Edo).
Sannan akwai Membobi da kuma wakilan hukumar a ma’aikatu da dama kamar yadda za ku gansu a cikin wadannan hotunan na kasa.
Wannan mukami da shugaban kasar ya bawa fitaccen jarumin yana nuni da cewa shugaban kasar bai mance da irin kokarin da jaruman masana’antar ta Kannywood suka yi masa ba a lokacin yakin neman zabe. Inda yawancin su suka fito kwansu da kwarkwatarsu suka goya masa baya.