BUHARI YA KI GAISAWA DA SARAKUNAN GANDUJE, SAI IYA SARKI SUNUSI
BUHARI YA KI GAISAWA DA SARAKUNAN GANDUJE, SAI IYA SARKI SUNUSI
Daga Rilwanu Labashu Yayari
An yi kallon-kallo tsakanin sarakunan jihar Kano a wurin taron yaye hafsohin ‘yan sanda da aka yi a garun Wudil na jihar.
A wuri taron ne sarakunan jihar Kano guda biyar suka fara haduwa da juna tun bayan kafa sabbin masarautu hudu a jihar.
Sarki Muhammadu Sanusi II ya isa wurin taron ne bayan sarakunan Bichi da Rano da Gaya da kuma Karaye, wadanda hakimai ne a masarautar Kano kafin kafin gwamnatin jihar ta nada su sarakunan yanka a sabbin masarautun da aka kirkiro a ‘yan watannin baya.
Sai dai sabbin sarakunan ba su gaisa da Sarki Sanusi ko sun yi magana da shi ko nuna sanayya ba har bayan taron.
Hakan ta sa aka yi mamaki, duba da dadaddiyar sanayyar da ke tsakaninsu da kasancewar dukkansu ‘yan majalisar masarautun jihar kuma manyan baki a wurin taron.
Wakilin BBC da ya halarci wajen ya ce yayin da Sarki Sanusi ya iske sauran sarakunan zaune a kusa da juna, tawagarsa ta iske wani basarake daga babban birnin tarayyar kasar Abuja, zaune a kujerar Sarki Sunusi a wurin.
Sakamakon haka ne aka ware wa sarkin wani wurin zama, abin da wasu ke gani a matsayin kaskantar da shugaban majalisar sarakunan jihar.
Bayan zuwan shugaban kasa Muhammadu Buhari taron, an sauya wa Sarki Sanusi wurin zama inda ya koma kusa da shugaban kasar a teburin da aka ware wa manyan bakin alfarma.
A karshen taron, shugaban kasar ya gaisa da Sarkin Kano Sunusi, amma sauran sarakunan ba su samu damar yin hakan ba, kasancewar Sarki Sunusi ne kadai a cikinsu yake sahun farko na manyan baki da ke kusa da shugaban kasar