Kannywood

Bilkisu Shema Ta Koka Kan Matsalar Tsaro A Katsina

Bilkisu Shema

MATSALAR TSARO: Fitacciyar Jarumar Kannywood Bilkisu Shema, ta bayyana takaicinta bisa halin da ƙanwarta da sauran wasu ɗalibai ke ciki a hannun ƴán bińdiga a jihar Zamfara.

Ta ƙara da cewa tun daga lokacin da wasu ‘yan bindiga suka sace ƙanwarta mai suna Hafsat Shema a makaranta dake garin Gusau a jihar Zamfara suka shiga tashin hankali.

Acewarta a ranar Larabar nan Hafsat ta kira gida inda take sanar da céwa tana kwance babu lafiya a cikin daji a hannun ƴán bindigar.

Saboda haka ne Bilkisu ke ƙara roƙon gwamnatin Najeriya, ta kara ƙoƙari domin kuɓutar da mutanen da ƴán bińdígar ke riƙe dasu a hannun su.

 

Back to top button
error: Content is protected !!