Bidiyon Jana’izar Nura Mustapha Waye Daya Rasu
Cikakken Bidiyin Jana’izar Daraktan IZZAR SO Nura Mustapha Waye Da Allah Ya Karfi Rayuwarsa, Innalillahi Wa’innaillahir Raji’un, Safiyar Ranar Lahadi Ne Muka Tashi Da Labarin Rasuwar Babban Mai Bada Umarni A Masana’antar KannyWood Kuma Mashiryin Shirin IZZAR SO. Wato Nura Mustapha Waye.
Inda Akayi Jana’izarsa Kamar Yadda Addinin Musulunci Ya Tanada. Jaruman KannyWood Da Dama Da Kuma Mutanen Gari Ne Su Sallaci Gawar Tashi Inda Bayan Anyi Sallah Aka Rakashi Zuwa Makabarta.
Masana’antar KannyWood Ta Shiga Alhinin Rashin Bawan Allah Domin Kuwa Ya Dade Yana Aiki Da Masana’antar, Zuwa Yanzun Jarumai Da Dama Sun Mika Da Sakon Ta’aziyyarsu Ga Iyalan Mamacin.
Mumq Daga Nan Shafin Mu Na HausaMini.Com Muna Mika Sakon Ta’aziyya Ga Iyalan Mamacin, Kuma Allah Ya Basu Hakurin Rashin Sa. Mu Kuma Allah Ya Kyautata Tamu Bayan Tashi Amin.







