(Bidiyo) Magidanci ya sauya sunan dansa da ya rada wa Buhari a 2015
– Wani magidanci a karamar hukumar Dutsinma ya sauya wa dansa suna daga Buhari zuwa Sulaiman
– An yi bikin da ya ja hankalin ‘yan Najeriya yayin taron bikin sauya sunan da aka yi a karshen makon jiya
– A farkon watan Disamba ne wani magidanci a Kano ya shirya biki bayan ya yi ikirarin cewa ya sauya sunansa daga Muhammadu Ibrahim zuwa Muhammadu Buhari
A karshen makon jiya ne wani biki ya yi matukar jan hankalin ‘yan Najeriya, inda wani mutum a jihar
Katsina ya sauya wa dansa suna bayan ya rada masa Buhari a shekarar 2015.
Mahaifin yaron, wanda tsohon masoyin shugaban kasa, Muhammadu Bihari, ne ya sauya wa dan nasa suna ne daga Buhari zuwa Sulaiman.
Da yake bayyana dalilinsa na sauya wa yaronsa suna bayan shekaru hudu da haihuwarsa, magidancin ya ce ya zabi sunan Sulaiman ne saboda tausayin da yake da shi ga mutane da dabbobi.
Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Dutsinma da ke jihar Katsina, jihar shugaba Buhari ta haihuwa.
A farkon watan Disamba ne wani magidanci a Kano ya shirya biki bayan ya yi ikirarin cewa ya sauya sunansa daga Muhammadu Ibrahim zuwa Muhammadu Buhari.
https://youtu.be/q9Nks_vrXPE