Baturen Daya Kawo Minning Ba Karamin Cutarmu Yayi Ba
Magana ta gaskiya batúrań da ya kawowa matasan mu labarin Crypto da Mining ba karamar cutar mu yayi ba, Cèwar Dr. Sheriff Almuhajir
Muna fama matasan mu su kama sana’o’i, har wasu sun fara yarda kawai sai ya sako musu kudin minning domin ya kara durkusar da tunanin su. Yanzu babu wata hujja da za ka bawa matashi ya yarda ya yaje sana’a tunda ya san idan ya zauna ya daddanna waya za’a bashi kudin kyauta.
Ni a gani na wannan ci baya ne, domin idan kowa ya koma sana’ar crypto to ya za’a yi kenan? Wa zai yi noma nan gaba, wa zai bude shago ko yayi kiwo tunda ya san idan ya danna waya za samu daloli kyauta.
Ni dai ina nan gefe zan noma shinkafa, idan sun baku kudin crypto sai ku zo ba kudin mu Saida muku shinkafa ku ci ko biya mu.
Masu karatu me za ku ce? Anya shima bai taro match da ‘yan Crypto ba kuwa ?