Bankin Masana’antu Zai Yi Wa ‘Yan Kannywood Bita A Kano
A Ranar Alhamis, Bankin Masana’antu (Bank of Industry, BOI) zai gudanar da taron bita (workshop) na rana ɗaya domin ‘yan Kannywood a Kano.
A takardar sanarwar taron wanda mujallar Fim ta samu, an nuna cewa za a fara taron da misalin ƙarfe 10 na safe a otal ɗin Bristol da ke Farm Centre.
Abubuwan da za a yi bitar a kan su su ne “Nigerian Film Business and Retrospect” (Nazari kan Kasuwancin Finafinan Nijeriya), “Industry Ecosystem” (Tsarin Yanayin Industirin Finafinai), “Industry Stakeholders” (Masu ruwa da tsaki a industiri), “Business of Film” (Kasuwancin fim), “Production” (Shirya fim), “Quality Assurance (Tabbatar da inganci), “Storytelling” (Ba da labari), “Cast & Crew” (Zaɓen jarumai da ma’aikata), “Content Monetisation” (Samun kuɗi da fim), “Physical and Digital Distribution” (Raba fim mutum da mutum da kuma a intanet) da kuma “Festivals” (bukukuwan baje-kolin finafinai).
Mutanen da aka tsara za su yi jawabai a taron sun haɗa da Chris Odeh, mamallakin kamfanin Sozo Films, Joy Odiete, mamallakiyar Blue Pictures Entertainment, Promise Ikechukwu George, shugabar guruf ɗin Creative and Digital Industries, jami’an Bank of Industry, da Alhaji Ibrahim Muhammad Mandawari, ciyaman Hukumar Amintattu ta ƙungiyar ‘yan Kannywood mai suna High Exhibition Film Professional Association (Kannywood).