E News

Bani Da Burin Daya Wuce Samar Da Zaman Lafiya Da Hadin Kai

Bani Da Burin Da Ya Wuce Na Samar Da Hadin Kai Da Zaman Lafiya A Najeriya Gaba Daya – BOLA TINUBU

– A Matsayina Ná Musulmí Da Na Yí Rantsuwa Da Alƙur’ani Maì Gírma Lokacìn Karɓar Mulkí Ya Zama Wajibi Ná Yi Shugbanci Na Adalci Ga Ko Wanne Sashe Na Kasar Nan, Céwar Bóla Tínubu

Shugaban ya bayyana cewa daga cikin manyan burukan da ya ke da su har ya nemi shugabancin Nageriya sun haɗa har da batun samar da haɗin kai da kuma zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasar.

“Mun sani cewa matsalolin rashin tsaro na da alaƙa da matsalolin rashin aikin yi da ƙarancin ilimi a tsakanin matasa, ina mai ba wa ƴan Nageriya tabbacin cewa su kara hakuri zamu yi nasara, zan wadata matasa da ƴan ƙasa da wadataccen aikin yi, kowa zai samu abin yi domin a gujewa tarzoma da ƙin juna, za mu samar da tsaro da zaman lafiya”.

Na tabbata zan dawo da Najeriya cikin hayya cinta, cèwar Shùgaban Kasa Alhaji Asiwaju Bola Ahmad Tinubu.

Tinubu ya ce yana da hanyar da za ta sake ɗaukaka Najeriya da kuma kawo ci gaba ga kowa da kowa, ya ƙara da cewa “Zan iya tafiyar da hanya zuwa wadata, na san hanyar ilimi domin na yi imani da shi, na san hanyar da za a magance matsalar rashin tsaro a kasar.”

Sai dai ya yi kira ga ƴan Najeriya da su ba shi damar yin aiki ta hanyar hakuri da taya shi addu’ar fatan yin nasara.

Ya ce, “Za mu yi aiki tare ne domin ba za mu koma lokacin da wasu ke sace kudin kasar ba, ba za mu bari a yi mulkin kama karya ba.”

Back to top button
error: Content is protected !!