Kannywood

Bani Bane Na Rasu. Mahaifiyata Ce – Jaruma Ladidi Tubeless

JARUMAR Kannywood, Sa’adatu Abdullahi, wadda aka fi sani da Ladidi Tubeless, ta bayyana cewa ba ita ce ta rasu ba, mahaifiyar ta ce.

Da ta ke yi wa mujallar Fim bayani, bayan yaɗa cewa Allah ya yi mata rasuwa jiya, Tubeless ta ce, “Ba ni ce na rasu ba, mahaifiya ta ce ta rasu kafin sallar Juma’a da misalin ƙarfe 12:00 na rana.”

A cikin kuka ta ci gaba da cewa, “Mama ta ƙawa ta ta ce, tunda na yi aure ni ban haihu ba, ita ce ‘ya ta, ita ce ɗa na, ita ce uwa ta, ita ce ƙawa ta – ‘she is my everything’!

“Ba zan iya kwatanta ta da komai ba. Ina son ta sosai, kuma ta san ina son ta, kuma ta na so na yadda na ke son ta. Ba ni da abin da zan iya haɗawa da ita.
“Yanzu ban san ya zan yi ba, saboda tun kafin ta rasu na kan ce mata, ‘Ran da ba ki ban san ya zan yi da rayuwa ta ba saboda son da na ke yi miki.’

“Yanzu da ta rasu ni ban san yadda zan yi da rayuwa ta ba.”

Hajiya A’isha Muhammad ta rasu a jiya Juma’a, 26 ga Janairu, 2024 a Asibitin 44, Kaduna, bayan ta yi fama da rashin lafiya da ta yi.

Dattijuwar ta rasu ta na da shekara 90 a duniya.

Ladidi Tubeless ita ce ‘yar ta ta 4.

An yi jana’izar ta da misalin ƙarfe 2:00 na rana, bayan an sauko sallar Juma’a, a layin Bashir Zubairu Birnin Gwari, Kabala Costain, Kaduna.

Ladidi Tubeless

Da dama daga cikin ‘yan Kannywood da kuma sauran mutane, musamman a soshiyal midiya, sun ɗauka cewa Tubeless ɗin ce ta rasu saboda yanayin yadda aka bada sanarwar rasuwar, ba a fahimta ba.

Allah ya jiƙan ta, ya albarkaci abin da ta bari, amin.

Fimmagazine.com

Back to top button
error: Content is protected !!