Banda Burin Daya Wuce Na Hada Kan Yan Nigeria
Ba Ni Da Burin Da Ya Wuce Na Samar Da Haɗin Kai Da Zaman Lafiya A Nageriya Gaba Daya – Cewar Shugaba BOLA Ahmad TINUBU
DAGA Bashir Abdullahi El-bash
Shùgaba Tinubù yace ita siyasa ba wai batu ne na shugabanci ba kawai, babban lamari ne akan sha’anin ilimi da ruhin al’umma da wayewar kan mutane da fahimtarsu da kuma aiwatar da daraja da tsare-tsare kyawawa.
Bola Tinubu yaci gaba da cewa Musulunci ya na koyar da mu kan mu cimma waɗannan ta hanyar da ta dace, waɗanda su ka haɗa da ba da shawara, da samar da mutane taurari abin koyi, da kykkyawan tunani da shugabanci nagari da sauransu. Manufar shugabanci a musulunci shi ne nusarwa da jagorantar al’umma kan ayyuka na kwarai da gujewa munana. Amana, gaskiya, adalci nagartocin musulunci ne da ake aiwatar da su a siyasa. Waɗannan kyawawan halaye daraja ce da ke kai shugaba ko ɗan siyasa ko duk wani bawa zuwa ga Aljanna ranar gobe ƙiyama.
A cikin Al”qur’ani mai girma, Allah maɗaukakin Sarki ya ce: “Sannan kuma mun sanya musu shugabanni a bayan ƙasa waɗanda za su riƙa jagoranci a bisa umarninmu; sannan kuma mun yi musu wahayi akan aiki na ƙwarai, da kula da Sallah da albishir da kykkyawan sakamako. Su ne bayi masu sadaukarwa a gare mu”. (Qur’an, 21:73).
Sai dai ya yi kira ga ƴan Najeriya da su ba shi damar yin aiki ta hanyar haƙuri da taya shi addu’ar fatan yin nasara.
Ya ce, “Za mu yi aiki tare ne domin ba za mu koma lokacin da wasu ke sace kuɗin ƙasar ba, ba za mu bari a yi mulkin kama karya ba.”
Wane fata zaku yi masa?