Labarai
Bance Kamal Aboki Bazai Samu Rahamar Allah Ba
Ba Ina Nufin Kamal Aboki Bazai Samu Rahamar Allah Bane, Kawai Dai Na Kawo Hadisi Ne Dake Nuni Da Cewa Wanda Ke Qirqiran Labarai Ayi Dariya, Bashi Ba Rahamar Allah. Malam Yayi Magana Bayan Mutane Sun Mishi Caa, Kan Martaninsa Na Rasuwar Kamal Aboki.
Wani Lamari Daya Dauki Hankula Bayan Rasuwan Kamal Aboki Shine Wani Gajeran Bidiyo Da Yake Yawo, Na Wani Malami, Da Yayi Wata Magana Na Cewa Duk Wanda Ya Mutu Yana Comedy, Bashi Ba Rahamar Ubangiji.
Wannan Ne Yasa Mutane Suma Malamin Diran Mikiya, Inda Suke Kai Tsaye Kawai Wannan Maganar Da Marigayi Kamal Din Yakeyi, Hakan Yasa Malam Ya Fito Ya Kare Kansa Daga Zage Zage Da Mutane Ke Masa.







