Labarai

Babu Dalilin Yin Zangazanga A Yanzu, Cewar Gwamnonin APC

Babu Dalilin Yin Zangazanga A Yanzu, Cewar Gwamnonin APC

Gwamnonin da aka zaɓa karkashin jam’iyyar APC mai mulki sun bukaci alumma suyi watsi da shirin gudanar da zanga-zanga suna masu cewa basu ga wani dalili da zai kai ga yin zanga zanga ba.

Shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ne ya bayyana haka lokacin da yake jawabi bayan wani taron da kungiyar gwamnoni APC ta gudanar a Abuja.

Yayi kira da masu shirya zanga zangar su zo a zauna a tattauna domin samun mafita.

Gwamnan Uzodimma ya ci gaba da cewa bai dace a halin yanzu ‘yan kasar nan su tsunduma cikin wata zanga-zangar da wata kungiya take shiryawa ba, inda ya bukaci ‘yan Nijeriya su yi watsi da zanga-zangar.

Ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya su yi hakuri da gwamnati, yana mai cewa ana ci gaba da kokarin ganin an daidaita matsalar tattalin arzikin da ake fama da ita a kasar.

Back to top button
error: Content is protected !!