Labarai

Babu Bukatar Warware Rikicin Masarautar Kano Da Karfin Iko

Babu Bukatar Warware Rikicin Masarautar Kano Da Karfin Iko Malaman Jihar Kano Ga Shugaba Bola Tinubu

Daga Lukman Aliyu Iyatawa

Malamai a Kano sun nuna damuwarsu kan abubuwan da ke faruwa a masarautar Kano inda suka bukaci Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta ɗaukar matakin da ya dace domin tabbatar zaman lafiya.

Malaman sun yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Majalisar Malaman karkashin jagorancin Shaikh Abdullahi Uwais Limanci.

Sun ce abubuwan da ke faruwa a Masarautar na baya-bayan nan za su iya rikidewa zuwa babban rikici idan ba a yiwa tubkar hanci ba.

Jihar Kano na ɗaya daga cikin Jihohin da suka fi zaman lafiya a Najeriya duk kuwa da sarkakiyar siyasar da ke faruwa a Masarautar a baya-bayan nan, wanda idan ba a yi taka tsantsan ba za ta iya rikidewa zuwa rudani, don haka ya zama wajibi Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dauki dukkan matakan da suka dace domin wanzar da zaman lafiya a Jihar.

Ya kamata shugaban kasa a matsayinsa na jagoran al’umma kada ya bari neman kujerar sarauta ta haifar da rikici. Muna kira ga maigirma shugaban kasa da ya baiwa al’ummar Jihar Kano damar warware waɗannan matsaloli cikin ruwan sanyi ba tare da yin amfani da karfin iko ba, wanda ka iya haddasa hasarar rayuka.

Jihar Kano na daya daga cikin jihohin da ke da zaman lafiya a Najeriya don haka a matsayin mu na jagororin Al’umma, muna kira ga bangarorin biyu da ke rikicin da su yi amfani da hanyoyin farar hula wajen warware sabanin da ke tsakaninsu domin samun zaman lafiya a Jihar.

Sanarwar tace, a matsayinmu na manyan masu ruwa da tsaki a Jihar muna so mu tabbatar wa Shugaban kasa cewa za mu tuntubi masu hamayyar domin bada gudummawar da za mu iya.

Allah Madaukakin Sarki Ya kawo mana zaman lafiya a Jihar mu da kasarmu baki daya.

Back to top button
error: Content is protected !!