Labarai

Babbar Kotu Ta Yi Watsi Da Tsige Sarki Aminu Ado Bayero

Babbar Kotu Ta Yi Watsi Da Dokar Da Ta Tsige Sarkin Kano Aminu Ado Bayero

Babbar kotun tarayya da ke Kano ta yi watsi da dukkan matakan da gwamnatin jihar Kano ta dauka na soke majalisar masarautar Kano, ta kuma yi fatali da dokar da ta tsige Sarkin Kano Aminu Ado Bayero.

Majalisar dokokin Kano ta soke dokar da ta samar da masarautu biyar a jihar, inda daga baya Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan sabuwar dokar da majalisar ta zartar tare da tsige, Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano.

Gwamnan ya rushe masarautu biyar da suka hada da Bichi da Rano Karaye da kuma Gaya da magajinsa, Abdullahi Umar Ganduje ya kirkiro.

Bayan tsige sarakunan, gwamnatin jihar ta dawo da Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II, wanda Ganduje ya tsige a shekarar 2020, a matsayin Sarkin Kano na 16.

Sai dai, Aminu Babba Danagundi, Sarkin Dawaki Babba, ya kalubalanci yadda aka aiwatar da dokar, inda ya bukaci kotun ta bakin lauyansa, Chikaosolu Ojukwu (SAN), ta soke dokar.

A hukuncin da ya yanke a ranar Alhamis, Mai shari’a Abdullahi Muhammad Liman, ya yi watsi da matakin da gwamnatin Kano ta dauka, inda ya umarci masarautun su ci gaba da zama daram.

Alkalin kotun ya ce wadanda ake tuhumar suna sane da umarnin wucin gadi da kotun ta bayar amma sun zabi yin watsi da shi kuma suka ci gaba da aiwatar da dokar.

Alkalin ya ce zai dauki karfin ikonsa na tilasta bin umarninsa.

Sai dai alkalin kotun ya mika karar zuwa ga mai shari’a Simon Amobeda domin ci gaba da sauraron karar zuwa kotun daukaka kara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!