Kannywood
Babanmu Kewa Sarkin Kano Shayi – Ado Gwanja
Fitaccen mawaki kuma dan wasan fina-finan Hausa na Kannywood, Ado Gwanja ya ce zai yi wuya ya kara aure kasancewar shi ‘kan-ta-ce ne’.
Ado Gwanja ya kuma shaida wa BBC irin matar da yake so ” ba doguwa ba, ba gajeriya ba kuma ba siririya ba ba mai kiba ba.”
Dangane da sana’ar gidansu da ya gada, ya ce ” ba don waka ba da watakila yanzu shayi nake sayarwa”, saboda a cewarsa mahaifinsa ne mai shayin Sarkin Kano.
“Idan Sarki zai sha shayi sai ya turo wurin mahaifina.”